Awori - Yarabawa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Awori - Yarabawa



Taswirar Tsibirin Lagos Kewaye da ruwa kamar yadda aka alamta da jan launi.
Hoto:Google Map

Gabatarwa

Awori, ɗaya ce daga cikin ƙabilun Najeriya wadda take cikin jinsin Yarabawa, waɗanda suka fi yawa a yankin Lagos da kuma wasu sassa na jahar Ogun.  Suna da ƙananan hukumomi goma sha uku a jahar Lagos da suka haɗa da Ikeja, Aliomosho, Mushin, Kosofe, Ifako-Ijaiye, Oshodi-Isolo, Somolu da kuma Agege. Sannan kuma su suke da manyan-manyan ƙananan hukumomin jahar Lagos da suka haɗa da Apapa, Eko (Wato asalin tsibirin Lagos), Lagos Mainland, Surulere, da kuma Eti-Osa. Haka nan kuma ana samun su a Ebute-Meta, Badagry, Iddo da sauran gurare masu muhimmanci. Sai kuma yankin Kudu-Maso Yammacin jahar Ogun musamman ma yankunan Isheri; gari mai matuƙar muhimmanci a tarihinsu, Ado-Odo, Otta da kuma Igbesa (Mann, 2007; Kotun, 1998; Durosinmi-Etti da tawagarta, 1998). 

Awori a Eko

Waɗannan marubuta, Mann, (2007); Durosinmi-Etta da tawagarta, (1998); Kotun, (1998); Adeyeri da Sanni (2012), sun bayyan cikakken labarin zuwan Awori wannan tsibiri na Lagos tiryan-tiryan da cewa:  Asalin kakan Awori, ɗa ne ga Oduduwa sannan kuma mafarauci mai suna Olofin Ogunfunminire wanda ya tashi daga garin Ile-Ife zuwa dajin Iseri (Isheri) gari mai tazarar kilomita 19.3 da Lagos ta Arewa wanda yanzu yake cikin Jahar Ogun.

Sun zauna zaman kusan kimanin shekaru talatin a garin Isheri abin da ya basu damar kafa wasu sababbin garuruwan waɗanda suka haɗa da Ota, Iro, Irenpa da sauransu.

Daga baya sun bar wannan yanki na Isheri tare da barin wasu birbishin su a gurin kamar yadda ya zo a ruyawar Durosinmi-Etta da tawagarta (1998), da cewa Awori sun canja sheƙa zuwa Ebute-Metta bisa dalilan tsaro. Daga baya da lamura suka sake ta’azzara a nan ma, sai suka sake canja sheƙa zuwa garuruwan Ota da Iddo. Inda shi madugu uban tafiya ya zauni garin da ake kira Iddo-Orille a bisa ruwayar Kotun (1998).

Zamowar garin Iddo katafariyar kasuwa da kuma tudun kamun kifi, mayaƙan sarkin Bini (Edo) suka matsantawa garin da hare-hare har ta kai ga sun kama Olofin Ogunfunminire tare da kawo ƙarshen rayuwarsa kamar yadda ya zo a ruwayar Durosinmi-Etta da tawagarta (1998), haka nan ma Kotun (1998). Sai dais hi Kotun ya bambanta da su game da maganar zama a Ebute-Metta inda ya ce kai tsaye daga Isheri suka tsallako zuwa Iddo garin da yaƙin ruwa ya taras da sakaina sannan ya ƙara da cewa kushewar Olofin Ogunfunminire tana nan a Iddo har zuwa yau ɗin nan.

Faruwar wannan yaƙi da kuma kisan shugaban Awori, Olofin Ogunfunminire, sai ‘ya’yansa da suka saura waɗanda suka haɗa da Olumegbon, Oloto, Oluwa, Onisiwo, Onitano, Ojora, Aromire, Elegushi da Oniru suka warwatsu zuwa guraren da suke ganin sun tsira da rayukansu suka ci gaba da rayuwa a gurin cikin kari da kuma zama lafiya, Durosinmi-Etta da tawagarta, (1998); Kotun, (1998). 

A wannan lokaci ne ɗaya daga cikin su, wanda shi ne Aromire ya tsallaka zuwa gefen tsibirin Lagos wanda ake kira Isale Eko, ya kafa gona yana noma jan-barkono sannan kuma yana kamun kifi da farauta sannu a hankali sauran jama’a suka zo suka taras da shi da jama’arsa kamar yadda aka bayanna dalla-dalla a wannan shafin.

To waɗannan zuriya ita ake kira Awori, kuma su ne dai ake cewa Omo-Eko da ma’ana ta ‘ya’yan Lagos masu gadon sarautar Lagos. Su jikokin Oduduwa ne ta gefen ɗansa Olofin Ogunfunminire wanda ya ƙaura da ga Ile-Ife zuwa Yankin Lagos amma ta gefen Iddo-Otto. Daga ƙarshe wannan gona ita ce ta zama gidan sarautar Lagos, wato Iga Idunganran.  

Manazarta


Adeyeri J.O. da Sanni H. A. (2012). Iba: Aspects of its Political History. LASU Journal of Humanities Volume 7, No. 1, January–June 2012. Faculty of Arts Lagos State University, Ojo Lagos, Nigeria.

Ajetunmobi R.O. (Babu shekarar wallafa). Aworin in View.

Durosinmi-Etti A.O. da tawagarta (1998). Welcome to Lagos Centre of Excellence, An Authoritative Guided Book on Lagos State of Nigeria. Royal Press Limited, Lagos.

Gatawa M.M. (2015).  The Role of Islam in the Yoruba-Hausa Harmonious Relations in Southwestern Nigeria. Department of History, Kaduna State University, Tafawa Balewa Way Kaduna Nigeria. IIUC Studies, ISSN 1813-7733, Vol.-12 December 2015 (P. 111-126). An ciro a shekarar 2020 daga shafin:  www.banglajol.info.index.php

Kotun B. (1998). The History of Eko Dynasty. Lagos State Ministry of Information and Culture.

Mann K. (2007). Slavery and the Birth of an African City Lagos, 1760–1900. Indiana University Press 601 North Morton Street Bloomington, IN 47404-3797 USA.

Sonuga G. (1987). Lagos State Life and Culture, Volume I. Lagos State Ministry of Information and Culture.



Sarakuna

  • Rilwanu Akiolu
  • Adeyinka yekani II
  • Adeniji Adele
  • Falolu
  • Esugbayi
  • Sanusi-Olusi
  • Ibikunle-Akitoye
  • Esugbayi
  • Oyekan
  • Dosunmu
  • Akintoye
  • Kosoko
  • Akintoye
  • Oluwole
  • Idewu Ojilari
  • Eshilokun
  • Adele Ajosun
  • Olugun Kutere
  • Eletu Kekere
  • Akinsomoyin
  • Gabaro
  • Ado

Kasuwanni


Bukukuwa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub