Sarkin Dutse Abdulƙadir

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Abdulƙadir Ɗan Salihu 1884 – 1893


Gabatarwa

Sarki Abdulƙadir shi ne sarki na talatin da huɗu a jerin sarakunan Dutse sannan kuma sarki na shida daga cikin sarakunan Fulani a Dutse. Shi ɗa ne ga Sarki Salihu (1807 – 1819) sannan kuma surukin Sarkin Kano Muhammadu Bello (1882 – 1893).  Ana yi masa laƙabi da Damamusau.

Bayan tsige sarkin Dutse Ibrahim (1868 – 1884), sai kuma sarkin Kano Muhammadu Bello ya naɗa surukinsa Abdulƙadir a matsayin sabon sarkin Dutse, dan ya samu cikakkiyar dama da kuma biyayya daga wannan masarauta ta Dutse.

Wannan naɗi na sabon sarki Abdulƙadir, ya zo a wani irin yanayin da wannan masarauta ta Dutse bata taɓa shigarsa ba. Sabon salon mulkin da shi sarkin ya zo da shi, na kakkaɓe hannun duk wanda yake zaton ba zai yi masa biyayya ba, da kuma dasa waɗanda ya ke sa ran samun goyon bayansu, ya haifar da rashin jituwa tsakanin gidajen da ke sarautar Dutse; wato Jalligawa da kuma Yalligawa.

Sarki Abdulƙadir ɗan Salihu ya rigayi Sarkin Kano Muhammadu Bello (1882 – 1893) rasuwa da wasu ‘yan watanni.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub