Sarkin Dutse Ada

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ada Gyauron Maza 1732 – 1735


Gabatarwa

Sarki Ada shi ne sarkin Dutse na ishirin da biyar. Tarihin sarakunan Dutse ba zai taɓa kammaluwa ba sai an saka shi. Shi ne sarkin da ya canza tarihin Masarautar Dutse. Shi mutum ne Bafulatani mai jarumtaka. Sarki Ada ya zo Dutse ne a matsayin shugaban rundunar mayaƙan Kano na zamanin Sarkin Kano Muhammadu Kumbari (1731 – 1743) dan hana sarkin Dutse Maƙuri (1720 – 1732) shiga ƙasar Kano dan kamo bayi da kuma bayar da kariya daga barazanar kawo hari daga Borno.

Bayan samun nasara da ya yi a yaƙin da suka gwabza da Sarkin Dutse Maƙuri (1720 – 1732), sai kuma ya ɗauki matakin da ya baiwa kowa mamaki shi ne na ɗarewa karagar mulkin Masarautar ta Dutse. Da ɗarewar tasa karagar mulki sai kawai ya mayar da hankali wajen haɗa rundunar yaƙi mai ƙarfi wacce ta juya tana yaƙar Masarautar Kano.

Sarki Ada ya samu nasarar faɗaɗa ƙasar Dutse ta hanyar mamaye wasu daga cikin sassan ƙasar Kano da suka haɗa da Aujara, Harɓo, Birnin-Kudu, Kiyawa da kuma Ringim sannan kuma ya jurewa dukkan wata turjiya da ya samu daga ubangidansa Sarkin Kano Muhammadu Kumbari (1731 – 1743) wanda ya tura shi ƙasar ta Dutse tun da farko.

Zamanin Sarki Ada shi ne farkon samun bunƙasar masarautar Dutse ta fuskacin siyasa da kuma tattalin arziƙi. Ya yi ƙarfin da ya zuwa shekarar 1735, babu wani mayaƙi daga tawagar Sarkin Kano Muhammadu Kumbari (1731 – 1743) da yake iya tunkararsa da yaƙi.

Wannan ƙarfi da ya samu, ya saka sarkin Kano Muhammadu Kumbari (1731 – 1743) haɗa wata runduna mai jarumawa casa’in da tara (99) da suka haɗa da sarkin jarumai Ayidajika, Barde Duguru, Ɗan’iya Tafiwa, Ɗan’iya Gajigi, Ɗantama, Ɗan’amar, Ɗankadai, Ɗan’akarya, Jambaɗe, Madawaki Yabo, Galadima, Ɗanfarmi, Sarkin Dawaki, Barde Sule, Jarmai Akalamu, Jarmai Tagwai, Ɗanhamoda, Ɗantankari Hamada, Ɗandama Kanwacilaya, Sarkin Gano Baƙo, Ɗantaratara, Ɗanmiskari, Ɗan’ashifa, Ɗangabu Baje, Ɗanlawan, Ɗanrimi, Ɗanmakwayo, Ɗanmaje, Ɗan’auta, Makaman Dal, Ɗanfari Zakari, Sarkin Sankara, Ɗan’ali Doka, Sarkin Bebeji Zakari, Sarkin Sakiya Atura, Sarkin Majiya Ɗandawa da sauransu.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub