Sarkin Dutse Akuli

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Akuli Gurumfa


Gabatarwa

Sarki Akuli Gurumfa shi ne sarkin Dutse na goma sha biyu. Shi ɗa ne ga sarki Dunhu. Sarki Akuli Gurumfa gwani ne wajen hawa doki. Sarki Akuli Gurumfa azzalumin sarki ne wanda ya wahalar da jama’arsa ta hanyar tursasa musu yin noma a gonarsa sannan kuma su biya haraji mai yawa ga nasu gonakin.

Sarki Akuli Gurumfa ya faɗaɗa masarautarsa ta hanyar cin garuruwan Gurum-Bayangari, Wurma, Dunduɓus, Buju, Daho, Abaya, ‘Yargaba da sauran garuruwa masu yawa waɗanda ke yamma da Garin Dutse.

Daga baya ya fice daga garin Garu ya koma Gurum-Bayangari bayan tuɓe shi a mulki da aka yi, inda a can ya ƙare rayuwarsa.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub