Sarkin Dutse Audu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Audu Idon Mikiya 1667 – 1679


Gabatarwa

Sarki Audu shi ne sarkin Dutse na ishirin. Shi ɗan’uwan sarki Habu ne ta ɓangaren uwa (wato mahaifiyarsu ɗaya da sarki Habu). Ana yi masa laƙabi da Idon Mikiya saboda ƙarfin gani da Allah ya yi masa. An ce idan ya hau Dutsen Ƙare Kallo zai iya bada labarin abubuwan da ke faruwa a nisan da ya kai wasu mila-milai. An ce wata rana ya taɓa tura mayaƙansa su tafi Dutsen Kila (yana da tazarar kilomita 30 daga Dutse) su farauto bayi sakamakon hayaƙi da ya hango yana tashi a kan Dutsen.

Salon mulkinsa ya bambamta da sauran, maimakon faɗaɗa ƙasa shi ya karkata ne wajen haɗa rundunar yaƙi mai ƙarfi saboda farautar bayi. Salon yadda yake kai hari tsakar dare ya matuƙar baiwa mutane mamaki game da ƙarfin ganinsa. A lokacin da ya rasu a cikin shekarar 1679, gawarsa ɓacewa ta yi daga cikin kabarinsa.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub