Sarkin Dutse Babilu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Babilu


Gabatarwa

Babilu Mai Karauna shi ne sarkin Dutse na bakwai. Shi jika ne a gurin sarakunan Dutse biyu; sarki Maigiji daga ɓangaren mahaifinsa, da kuma sarki Maido daga ɓangaren mahaifiyarsa. Shi mutum ne jarumi kuma mai son kwalliya da mata. A lokacin da ya rasu ya bar mata bakwai, dawakai bakwai, sutura bakwai, takubba bakwai, kibau bakwai a cikin kurtunsu, da kuma takalma bakwai.

Shi ma ya ƙware wajen hulɗa da iskokai. Shi ne sarkin da ya mayar da hulda da iskokai ta zama gama-gari. Ya wakilta abokinsa na ƙut-da-ƙut mai suna Dodan Yaron-Maigiji ya zama mai kula da hidimar da sauran jama’a ke yi wa iskokai tare kuma da karɓar kyaututtukan da jama’ar ke yi wa iskokan. Da yamma yakan hau Dutsen Ƙare Kallonka yana kula da ƙasa.

Shi mutum ne mai kamen bayi. Yakan fita ƙauyuka ya ratattake su ya kama bayi. Ya kan tafi har Dutsen Kila ya kamo bayi. A garin Zai yake ajiye bayin nasa. Yana amfani da waɗannan bayi wajen noma kayan amfanin gona da kuma yaƙi.

Sarki Babilu ya rayu a kusa da ƙoramar Karauna wacce ruwanta ke kwararowa daga kan dutse. Ya mulki masarautar Dutse tsawon shekaru goma sha bakwai.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub