Sarkin Dutse Bello

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Bello Ɗan Musa 1840 – 1849


Gabatarwa

Sarki Bello shi ne sarki na talatin da ɗaya a jerin sarakunan Dutse sannan kuma sarki na uku a jerin sarakuna Fulani a Dutse. Sarki Bello ɗa ne ga Sarkin Dutse Musa (1819 – 1840) sannan kuma jika ga galadiman Kano Sani ta ɓangaren mahaifiyarsa.

Sarki Bello mutum ne jarumi. Bayan hawansa karagar mulki, ya yi fama da rikicin cikin gida kasantuwar wasu daga cikin ‘yan’uwansa suna ganin cewa tasirin zamowar mahaifiyarsa ‘yar wani daga cikin masu mulkin Kano shi yasa aka danƙara musu shi a matsayin sarki. Saboda haka sai suka ƙi yi masa biyayya suka goyi da bayan Sulemanu wanda shi kuma mahaifiyarsa ‘yar Sarkin Dutse Gwajabo (1799 – 1807) ce.

Sarki Bello ya yi nasarar warware wannan matsala ta cikin gida, sannan kuma ya ƙaddamar da hare-hare a ƙoƙarinsa na ƙwato ƙasar da ta sake kuɓuce wa Dutse bayan nasarar da Sarki Ada (1732- 1735) ya yi a kansu. Ya yaƙi garuruwa irin su Gaya, Ajingi, da Aujara waɗanda duk suke cikin ƙasar Kano. Bayan yaƙar wani ɓangare na ƙasar Kano da ya yi, sai kuma ya ma ƙi baiwa ƙasar Kano harajin yaƙi kamar yadda aka yi yarjejeniya da magabatansa.

Faruwar wannan al’amari sai ta saka sarakunan Kano suka yaudare shi suka gayyace shi a matsayin ɗangida ya je taron tattaunawa na iyali a zamanin sarkin Kano Usman Ɗan Dabo (1846 - 1855). Suka kwantar masa da hankali suka nuna masa cewa so suke a yi ‘yar cikin gida, a yi sulhu, su haɗa ƙarfi waje guda, an yi wannan a cikin shekarar 1849. Da isarsa Fadar Masarautar Kano aka karɓe shi hannu biyu-biyu, aka zaunar da shi a kan wata shinfiɗa da aka yi a kan rami wanda yana zama ya rufta ciki. Raunukan da ya samu a wannan faɗawa rami su suka zamar masa ajali kamar yadda ya zo a Sanusi (2009).  

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub