Hakimin Dutse Bello II

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Bello Ɗan Abdulƙadir 1919 – 1923 (Hakimi)


Gabatarwa

Bello Ɗan Abdulƙadir Bajallige, shi ne ya gaji sarki Abdullahi Bayallige. Shi ya zamo hakimin Dutse na biyar. Naɗin da sabon Sarki Kano Usman Ɗan Abdullahi (1919 - 1926) ya yi masa.

Bayan wannan naɗi nasa ne Turawa a ƙoƙarinsu na horas da jama’ar Dutse game da boren da suka yi musu, sai suka sake tsuke wannan masarauta ta Dutse ta tashi daga yankin hakimi ta koma digaci, matakin da ‘ya’yan sarautar ta Dutse suka sake bijirewa. A wannan sabon naɗi da aka yi, an saka ita masarautar ta Dutse ƙarƙashin kulawar Ɗan-Lawa ɗin Kano Umar Yola. Shi kuma sarkin Dutsen aka taƙaita masa ɗawainiyoyinsa suka tsaya iya Garu.

Wannan mataki ma dai da Turawa suka ɗauka bai haifar musu da ɗa mai ido ba, maimakon haka ma sai su gidajen sarautar Dutse suka kalle shi a matsayin yunƙurin tursasawa Dutse ta koma ƙarƙashin ikon Kano baki ɗaya. Saboda haka sai suka bijire tare kuma da taurarewa a kan bijirewar tasu. Yanayi ya yi tsamarin da shima Ɗan-Lawan ɗin ya kasa karɓar haraji.

Amma duk da haka shi Rasidan ɗin Dutse yana kallon cewa fa, lallai ita Masarautar ta Dutse tana da girman da ta kai a raba ta biyu, amma duk da haka ya kau da kai saboda dalilan tattalin arziƙi. Shi kuwa jami’in mulki na yankin Dutsen, Mr. Nor, sai ya ƙara tabbatarwa da shi Rasidan cewa lallai za a raba Dutse gida biyu.

Lamari ya tsaya cik a Dutse, zaman Ɗan-Lawan ya gagara a Dutse, haka nan shi ma sabon Sarkin ya kasa taɓuka komai. Saboda haka sai aka cire shi a shekarar 1922, wanda daga nan ya yi hijira zuwa Katanga inda ya rasu a can a shekarar 1923.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub