Sarkin Dutse Dunhu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Dunhu


Gabatarwa

Dunhu Ɗan Maryama shi ne sarkin Dutse na Goma sha ɗaya. Shi Dunhu ɗa ne ga Maryama matar marigayi Sarki Sambore. Saboda haka shi agolan Sarki Sambore ne.

Maryama kuma Babarbariya ce, mahaifinta shi ne wanda ya fara zama a wannan yanki na Maremawa. Saboda haka bayan rasuwar mijinta Sarki Sambore, sai ta fice daga garu ta koma cikin ‘yan’uwanta Maremawa wanda kuma shima sabon sarki ya bita can ya ci gaba da gudanar da mulkinsa a garin na Maremawa. A iya tsawon mulkin Sarki Dunhu, mahaifiyarsa ta kasance mai tsananin ƙarfin faɗa-a-ji a cikin harkokin mulki wanda hakan kuma bai yi wa mutane da dama daɗi ba, saboda haka jama’a suka tursasa masa yin murabus biyowa bayan wani matsanancin fari da aka yi wanda ya sabauta mutuwar dabbobi da dama. Sannan suka naɗa ɗansa. Sarki Dunhu ya mulki Masarautar Dutse tsawo

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub