Sarkin Dutse Hassan

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hassan Makau Dodon Bango 1686 – 1702

Gabatarwa

Sarki Hassan shi ne sarkin Dutse na ishirin da biyu. Shi ɗa ne ga sarkin Dutse Audu Idon Mikiya (1667 – 1679). Ana kiransa da sunan Dodon Bango saboda Imani da jama’arsa suka yi cewa, yana iya ratsa bango komai kaurinsa ya wuce ba tare da bangon ya tsage ba (wato siddabarun nan da ake kira Bi-Bango). Yana da tsubbace-tsubbace masu tarin yawan waɗanda suka haifar da tsoro a zukatan jama’arsa wanda haka ta saka suka bishi ba dan sun so ba.

Yakan saka layu da guraye masu mabambamtan girma a wuyansa da ƙugunsa wanda hakan kan haifar da tsoro a zukatan abokan adawarsa. Ya rasu a cikin shekarar 1702 sakamakon wata rashin lafiyar da ta biyo bayan bikin shekara-shekara da suke yi na hidima a Dutsen Asarki.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub