Sarkin Dutse Ibrahim

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ibrahim Ɗan Salihu 1868 - 1884

Gabatarwa

Sarki Ibrahim shi ne sarki na talatin da uku a jerin sarakunan Dutse sannan kuma sarki na biyar a jerin sarakunan Fulani. Shi ɗa ne ga sarkin Dutse malam Salihu Ɗan Ibrahim (1807 – 1819) Bajallige, sannan kuma surukin Sarkin Kano Abdullahi Ɗan Dabo (1855- 1882).

Sarkin Kano Abdullahi Ɗan Dabo (1855- 1882) shi ya naɗa sarki Ibrahim Ɗan Salihu wanda ake yiwa laƙabi da Irema a matsayin sabon sarkin Dutse bayan rasuwar sarkin Dutse Suleman Ɗan Musa (1849 – 1868) Bayallige.

A zamanin sarki Ibrahim dagantaka tsakanin Kano da Dutse ta ƙara kyautatuwa duk da cewa ko kusa ba za a iya misalta ta da zamanin Sarki Sulemanu Ɗan Musa (1849 – 1868) ba, saboda kwarjinin da shi marigayin sarkin yake da shi.

Wannan kusanci da aka samu tsakanin sarkin Kano Abdullahi Ɗan Dabo (1855- 1882) da sabon Sarkin Dutse Ibrahim Ɗan Salihu ita ta zamewa sabon sarkin matsala daga baya, a lokacin da sabon sarkin Kano Muhammadu Bello (1882 – 1893) ya fara tsige manya-manyan shuwagabannin da yake ganin masu bin tsohon sarki ne sau-da-ƙafa. Ya umarci sarkin Dutse Ibrahim da ya saki matarsa Fulani Ayyah wacce take ‘ya ce ga marigayi sarki Kano Abdullahi Ɗan Dabo (1855- 1882) a matsayin sharaɗin da zai tabbatar masa da sarautarsa, amma duk da haka bai tsira ba.

Daga baya an tuhume shi da ɓarnatar da dukiyar al’umma da kuma rashin biyayya ga sarkin Kano Muhammadu Bello (1882 – 1893). Bayan watanni uku kuma sai aka janye waccar tuhuma, sannan aka tura shi zuwa Wurma dan gudun hijira. Daga baya kuma shi sarkin Kano Muhammadu Bello (1882 – 1893) ya rubuta wasiƙa a cikin shekarar 1884 ya tura zuwa ga Wazirin Sakkwato yana mai sanar da shi matakin da ya ɗauka a kan sarkin Dutse Ibrahim Ɗan Salihu da kuma dalilansa na aikata hakan.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub