Sarkin Dutse Inuwa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Inuwa Bagizire 1643 – 1658

Gabatarwa

Sarki Inuwa shi ne sarkin Dutse na goma sha takwas a jerin sarakunan Dutse. Shi aboki ne kuma suruki ga sarkin Dutse Yakubu. Ya auri ɗaya daga cikin ‘ya’yan sarki Yakubu. Sarki Inuwa Babarbare ne wanda iyalansa ke zaune a garin Gizirawa wani ɗan ƙaramin gari da Duna Magu ya kafa; maharbin da ya sakawa Dutse sunan Gadawur.

Sarki Inuwa mutum ne mayaƙi, shi ne sarkin Dutse da ya fara amfani da bindiga da kuma rigunan lifida a fagen yaƙi. Shi ya baiwa jama’ar Masarautar Dutse kariya da kuma sake dawo da waɗanda suka fanɗare a zamanin marigayin sarki.

Ya gina fadar mulkinsa a saman Dutsen da ke garin Gizirawa saboda ya riƙa hango garuruwan da ke kudu da shi da kuma garin Garu da ke yamma da shi.

Sarki Inuwa ya rasu a shekarar 1658 sakamakon rauni da ya samu a lokacin yaƙinsa da Gaya a yunƙurinsa na kare ƙasarsa.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub