Sarkin Dutse Labun

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Labun


Gabatarwa

Labun ɗa ne ga sarkin Dutse Babilu. Shi ne ɗansa na farko. Ya zamo sarkin Dutse na Takwas bayan rasuwar mahaifinsa. Shi mutum ne matsafi kuma mai tsananin camfi, sannan kuma mai son rayuwar kaɗaitaka. Kusan a Dutsen Achiza ya gudanar da rayuwarsa ta son kaɗaici. A wannan Dutse na Achiza ya ke ganawa da nasa iskokan maimakon Dutsen Asarki. A zamaninsa ya tursasa jama’a yin rantsuwa da iskokan da ke Dutsen Achiza.

Yakan yi ado da rawani shuɗi mai baƙi-baƙi wanda aka yi wa ƙyale-ƙyale da layu. Wuyansa kuma da kafaɗarsa yakan yi musu ado da asalin kayan ƙyale-ƙyale na mata.

Shi ya assasa wasan Dodo da ake yi shekara-shekara. A wannan dutse yake ganawa da iskokai wajen neman gudunmawarsu a kan abubuwan da suka shafi jama’a kai tsaye kamar neman waraka daga kowace irin nau’in cuta.

Shi ya ‘yanta bayin da ya gada daga magabatansa, sannan kuma ya mallaka musu gonaki ya kuma basu damar yin dukkan abubuwan da asalin ‘yan ƙasa suke yi kamar noma. Ya yi sarauta ta tsawon shekaru goma sha uku.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub