Sarkin Dutse Maidoi

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Maido


Gabatarwa

Sarki Maido ɗa ne ga Sarki Tuwai Mai Asarki Babba ta ɓangaren mahaifiyarsa. Wato shi ɗa ne ga Ƙorama, wacce ita kuma ‘ya/ɗiya ce ga sarkin Dutse Tuwai Mai Asarki Babba. Haka nan kuma mahaifinsa ɗaya ne daga cikin ‘yanmajalisar sarki, sannan kuma yardajjen abokin sarkin Dutse Tuwai.

Sarki Maido ya rayu a yankin Asarki Ƙarama, kuma ya kasance mai yawan hulɗa da iskokai sannan kuma yana yi musu hidima da mushen dabbobi. Jama’arsa sun dogara da shi sannan kuma suna yarda da duk abin da ya faɗa musu dangane da annoba ko wanin haka nan. Ya riƙa ƙarfafawa jama’ar gari guiwa wajen neman taimakon iskokai dangane da abubuwan da suka shafi samun waraka daga rashi, taɓin hankali, bugun aljanu da sauransu ta hanyar yi wa iskokan hidima.

Ya yi amfani da wasu dabarbarunsa wajen tsorata jama’a da annoba ta hanyar harsashe da yake yi sannan kuma ya nuna musu idan basu yi abin da iskokan ke buƙata ba to suna cikin hatsari. Kodawane lokaci yana cikin duwatsun Asarki, yana roƙa wa jama’a kyakkyawar rayuwa, lafiyar jiki, da kuma yalwar abinci a wajen iskokai. Ya yi sarauta ta tsawon shekaru shida.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub