Sarkin Dutse Maigiji-Tandu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Maigiji-Tandu


Gabatarwa

Maigiji-Tandu bai gaji sarauta ba, sai dai shi ɗa ne ga wani attajiri wanda ke da dukiyar dabbobi. Maigiji-Tandu shi yake samar da nono awaki ga jama’ar gari. Yana da wata dabara ta adana nono na tsawon lokaci ta hanyar zuba wasu ciyayi a ciki.

Maigiji-Tandu ya zamo sarkin Dutse na biyar bayan rasuwar Sarki Maido saboda yawan dukiyarsa da kuma zamowar ‘ya’yan marigayin sarkin ƙanana.

A zamaninsa ya nisanta jama’a daga yawan dogaro da iskokai ya kuma ƙarfafa yin aiki tuƙuru wajen samun abin masarufi.

A zamanin sarkin Dutse Maigiji-Tandu aka samar da marinar da ke garin Limawa da Kachi waɗanda suka zama ƙari a kan waɗanda ake da su a Birnin Gija. Tattalin arziƙin jama’ar yankinsa ya matuƙar bunƙasa musamman ma garin Garu.

Sarki Maigiji-Tandu ya rayu a ƙarƙashin dutsen Tandu da ke unguwar Alƙalawa a cikin garin Tsakuwa. Wannan dutse ya samu wannan suna ne daga sunan sarkin.

A cikin shekarar 1489 aka samu wata annobar gobara wacce ta yi sanadiyar halakar rayuka da dama da kuma ɗimbin dukiyar da ta haɗa da gidaje, dabbobi, da sauransu. Faruwar wannan annoba ya sake ƙarfafawa jama’a guiwa game da imaninsu da dangantakar da ke tsakanin tsohon sarki mai rasuwa, sarki Maido da iskokai.

Sarki Maigiji-Tandu ya yi murabus daga kujerar sarautar Dutse bayan da ya samu tursasawa daga mutanensa kan dole ya bar gadon mulkin. Bayan barinsa sarautar ya ƙaura zuwa garin Yina inda a can ya rasu. Sarki Maigiji-Tandu ya zauna a gadon mulkin Dutse na tsawon shekaru bakwai.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub