Hakimin Dutse Maikano

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Abdullahi Maikano 1960 – 1983


Gabatarwa

Sarki Abdullahi Maikano Bayallige, shi ne babban ɗan Sarki Suleman II (1923 – 1960). An haife shi a shekarar 1915, a garin Kano. Dalilin da ya saka ake yi masa laƙabi da Maikano.

Ya yi karatunsa na firamare a makarantar Elimantare da ke Gidan Ɗanhausa a cikin unguwar Nassarawa, a Kano. Daga nan kuma ya samu nasarar ci gaba da karatu a shahararriyar makarantar nan ta Katsina; wato Kwalejin Horas da Malami ta Katsina (Katsina College).

Bayan gama karatunsa ya yi aiki da Hukumar Gargajiya (Native Authority) ta Kano a matsayin Wakilin Asibiti (Head of Health Department). Ya kuma riƙe muƙamin Ministan Ƙanan Hukomomi da Ci Gaban Al’umma na Yankin Arewa (Northern Region Minister for Local Government and Community Development) daga shekarar 1957 zuwa 1960. Sannan kuma shi ya zama ciyaman na farko na jama’iyyar NPC na Lardin Kano (NPC Chariman Kano Province), sannan kuma ya riƙe muƙamin Mai Tsawatarwa na Zauren Majalisar Arewa (Chief Whip, Northern House of Assembly).

Ranar 15 ga watan Agusta na shekarar 1960, aka yi masa naɗin da ya mai da shi Hakimin Dutse na bakwai, daga baya kuma ya zama Sarkin Dutse na talatin da tara a jerin sarakunan Dutse, sannan kuma sarki na goma sha ɗaya a sarakunan Fulani. Naɗinsa ya biyo bayan rasuwar mahaifinsa Sarkin (Hakimi) Dutse Sulemanu II (1923 – 1960).

A zamaninsa aka gina Babbar Makarantar Firamare (Dutse Senior Primary School) ta Dutse a cikin shekarar 1960 a garin Takur. Sannan kuma a zamaninsa ne aka yiwa Dutse helikwatar Ƙaramar Hukumar Dutse a shekarar 1976.  Sannan kuma dai a zamaninsa ne aka samar da titin da ya fara daga Kwanar Fuguma ya wuce zuwa Yadi, sannan ya zarce har Kiyawa.

A ranar 1 ga watan Afirilu na shekarar 1981, masarautar Dutse tare da wasu masarautun da suka haɗa da Gaya, da Rano da kuma Auyo daga masarautar Haɗeja aka sake ɗaukaka darajarsu zuwa masarautun yanka a zamanin Gwamnan Kano Marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi. Bayan wannan ne kuma a ranar 5 ga watan Juli na shekarar 1981, Sarki Abdullahi Maikano ya zama sarki mai daraja ta ɗaya, matsayin da ya ɗaukaka darajarsa sama da ta Haɗeja da Kazaure.

Kwan-gaba-kwan-baya, kwatsan bayan shekara biyu da watanni huɗu da wannan naɗi nasa a matsayin sarkin yanka da kuma ɗaukaka darajar yankin Dutse zuwa Masarautar Yanka wanda shi ta ke a kai tun asali, sai sabon Gwamnan Kano, Alhaji Muhammadu Sabo Bakin Zuwo ya sake tsuke wannan masarauta tare da abokan naɗinta zuwa yankin hakimi a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1983.

Faruwar wannan al’amari ta saka Sarki Abdullahi Maikano yin murabus. Daga nan kuma ya ƙaura zuwa Hotoro da ke Kano, inda ya ƙarasa rayuwarsa a can.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub