Sarkin Dutse Maisaje

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Mamman Maisajen Fama 1702 – 1720


Gabatarwa

Sarki Mamman Mai Sajen Fama shi ne sarkin Dutse na ishirin da uku. Shi mutum ne jarumi wanda ya ƙware wajen yaƙi. Wannan dalilin ne ma ya saka aka yi masa laƙabi da Mai Sajen Fama.

Rubutaccen tarihi ya tabbatar da bunƙasar Masarautar Dutse tun kafin zamowarsa sarki (Sanusi, 2009). Ya zuwa lokacin mulkinsa Dutse na da garuruwa goma sha bakwai da suke killace a cikin ganuwarta wacce ke da ƙofofi goma sha biyu da ake ambatar kowace ɗaya da sunan gari mafi kusa da ita kamar haka:

 1. Ƙofar Maranjuwa.
 2. Ƙofar Burtilan.
 3. Ƙofar Yina.
 4. Ƙofar Ƙoƙiya.
 5. Ƙofar Bukka.
 6. Galamawa.
 7. Ƙofar Ma’ai.
 8. Ƙofar Tago.
 9. Ƙofar Kachi.
 10. Ƙofar Gadadin.
 11. Ƙofar Galadimawa.
 12. Ƙofar Rariya.

Duk da cewa waɗannan Ƙofofi sun ɓace, amma har yanzu akan samu sauran abin da ba a rasa ba na daga ɓuraguzan wasu daga ciki. Sarki Mamman Mai Sajen Fama ya rasu a Fagen Fama a lokacin da yake tallafawa Kano dan ta yaƙi Zamfara a zamanin Sarkin Kano Muhammadu Ɗan Daɗi (1703 – 1731).

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub