Sarkin Dutse Mamman

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Mamman Tauroma 1616 – 1632


Gabatarwa

Sarki Mamman Tauroma shi ne sarkin Dutse na goma sha shida. Shi makusanci ne ga sarkin Dutse Yusufu. Mutum ne maɗinki. Saboda son kwalliyarsa ake yi masa laƙabi da Mai Babban Wando.

Bayan zamowarsa maɗinki, sarki Mamman kuma manomi ne, saboda wannan dalilin ne ma ya gina gida a gefen ƙoramar Jambo dan ya samu damar yin aikinsa na lambu a lokutansa na hutawa.

Zamanin Sarki Mamman yaƙi ya yi sauƙi, sannan kuma harkar noma ta haɓɓaka. A zamaninsa ya rage yawan harajin da ake karɓa a hannun manoma. Shi ne ya samar da kasuwar nan ta Limawa.

Sarki Mamman bai damu da dukiyar jama’a da ke baitil mali ba, ya ma kasance yana tallafar tattalin arziƙin masarautar da tasa dukiyar. Ya rasu a shekarar 1632 sakamakon cutar kuturta.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub