Sarkin Dutse Mani

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Mani Mai Artabu 1679 – 1686


Gabatarwa

Sarki Mani shi ne sarkin Dutse na ishirin da ɗaya. Shi ɗa ne ga sarkin Dutse Inuwa Bagizire (1643 – 1658).  Mutum ne mayaƙi. Ƙwarewarsa wajen yaƙi da kuma shaharar da ya yi wajen yaƙi a kusa da nesa, shi ya saka aka yi masa laƙabi da Mai Artabu. Mutum ne garjeje, kallonsa na firgita maza idan hankalinsa ya tashi saboda girman kafaɗarsa da kuma kwarjinin idanuwansa. Yana da dabarar yaƙi da nacewa wajen kai hari kan abokan gaba, saboda a ganinsa barin abokin gaba ya huta to zai samu cikakkiyar damar yin tunanin ya sake shiri babban kuskure ne.

A zamaninsa ya fara faɗaɗa ginin ganuwar Dutse. Ya fara gini daga Gizirawa, zuwa Ihunka-Banza kusa da Jigawar Saki sai kuma ya rasu.

Sarki Mani ya rasu a cikin shekarar 1686 a garin Dutse Danga da yanzu yake cikin ƙaramar Hukumar Ningi ta Jahar Bauchi, a lokacin fafatawarsu da Ningawa a yunƙurinsa na tallafawa sarkin Kudu ya ƙwato ƙasarsa daga hannun Ningawa. Kuraye suka cinye gawarsa tare da sauran gawarwakin yaƙin.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub