Sarkin Dutse Mantau

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Mantau Jarmai Babba 1577 – 1584


Gabatarwa

Sarki Mantau shi ne sarkin Dutse na goma sha uku. Sarki Mantau jarumin mutum ne mayaƙi, saboda haka ne ma aka yi masa laƙabi da wannan suna na Jarmai.

Masarautar Dutse ta samu ci gaba mai amfani a zamanin Sarki Mantau Jarmai. Ya faɗaɗa masarautar Dutse ta sashen Arewa da Gabas ta hanyar sulhu. Daga gabas da Dutse an samu garuruwa irin su Garko, Tsurma, Abalago, Katuka, Kiyawa, Kwanda, Tarho, Katanga da kuma Fake duk sun yarda sun koma ƙarƙashin masarautar Dutse. Haka nan ma ta ɓangaren Arewa ya narkar da wasu garuruwan sun koma ƙarƙashin marautarsa ta Dutse ta hanyar sulhu maimakon yaƙi.

Sarki Mantau ya samar da ingantaccen yanayin tattalin arziƙi da kuma siyasa a wannan masarauta ta Dutse, sannan kuma ya mayar da noma a gandun sarki (gonar sarki) ba bisa tursasawa ba. Wato kenan bisa ganin dama ake zuwa noma gandu sarki.

Sarki Mantau ya mulki Masarautar Dutse tsawon shekaru bakwai. Ya rasu a filin daga lokacin yaƙin Kwararrafa.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub