Sarkin Dutse Amadu Maranje

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Amadu maranje



Me ka ke nema?


Gabatarwa

Amadu Maranje shi ne sarkin Dutse na shida. Kamar sarki Maigiji-Tandu, shi ma Amadu Maranje ba shi da wata danganta ta jini da gidan sarautar Dutse. Sarki Amadu Maranje babban manomi ne, shi yake noma mafi yawan abincin da jama’ar wannan yanki suke amfani da shi. yakan baiwa jama’a hatsi shi kuma ya karɓi dabbobi a hannunsu. Ya kasance yana noma shinkafa a rafin Tsatiya, sauran dangogin hatsi kuma a kan jigawar Maranjuwa.

Garin Maranjuwa ce fadar mulkin sarki Amadu Maranje. Shima masanin hulɗa da iskokai ne kamar sarkin Dutse Maido wanda wannan yana daga cikin dalilan da suka ba shi damar zama sarkin Dutse bayan afkuwar waccar annoba da ta sabauta murabus ɗin sarkin da ya gabace shi.

Sarkin Dutse Amadu Maranje shi ya sake gina fadar masarautar Dutsen da ke Garu. Dan ya cimma wannan buri nasa na sake gina Garin Garu, sai da ya riƙa yawan zuwa dutsen Asarki saboda ganawa da iskokai tare kuma da yi musu hidima da dabbobi masu tarin yawa. Lokacin da buƙatarsa ta samu karɓuwa a wajen waɗannan iskokai, an ga hayaƙi ya turnuƙe kewayen gurin abin da ke alamta samun karɓuwar buƙatar tasa a wajen iskokan.

Wannan al’ada ta hulɗa da iskokai kuma sai ta samu gindin zaman da bata gushe ba har sai da Fulani masu jihadi suka bayyana a shekarar 1807. Sarki Amadu Maranje ya yi sarautar Dutse ta tsawon shekaru tara.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub