Sarkin Dutse Musa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Musa Ahmadu 1819 – 1840


Gabatarwa

Sarki Musa shi ne sarki na talatin a jerin sarakuna Dutse sannan kuma sarki na biyu a jerin sarakuna Fulani a Masarautar Dutse. Shi sarki Musa ya fito daga Fulani Yalligawa saboda haka shi Bayallige ne. Sarki Musa abokin sarkin Kano ne Malam Ibrahim Dabo (1819 – 1846) saboda kasancewarsa masanin dabarun yaƙi kuma jarumi.

Naɗinsa a matsayin sarkin Dutse ya biyo bayan ɗarewa kujerar sarautar Kano da Malam Ibrahim Dabo (1819 – 1846) ya yi ba da jimawa ba. Jarumtakarsa da dabararsa sun bayyana bayan samun galabar da aka samu a kan Birnin-Kudu a zamanin Sarki Salihu (1807 – 1819) da kuma aurensa ga ‘yar sarkin Dutse Gwajabo (1799 – 1807) da kuma ‘yar galadiman Kano.

Haka nan kuma dabarar yaƙin nasa ta ƙara bayyana bayan galabar da ya samu a kan baraden daular El-Kanemi ta Borno a garin Fake a shekarar 1826. A zamaninsa Masarautar Dutse ta shahara a wajen yaƙi. Ya samu galaba a yaƙoƙi da dama da ya yi.

Ya bar kujerar mulki a shekarar 1839 bayan cutar makanta da ta kama shi ya samu raunin gani. Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo (1819 – 1846) ya umarce shi da ya bada sunan wanda yake ganin zai gaje shi sai ya bada sunan babban ɗansa ciroman Dutse Sulaiman. Amma daga ɗaya gefen kuma sai surukinsa Galadiman Kano Sani ya bayar da sunan jikansa Bello. Saboda wannan dalilin sai shi Sarkin Dutse Musa Ahmadu ya zaɓi ya fice daga garin. Ya yi ƙaura zuwa garin Shira wacce ke cikin Masarautar Katagum inda ya zauna har zuwa shekarar 1843.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub