Sarkin Dutse Salihu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Salihu Ɗan Ibrahim 1807 – 1819


Gabatarwa

Sarki Salihu shi ne sarki na ishirin da tara a jerin sarakunan Dutse sannan kuma sarki na farko a jerin sarakunan Fulani. Shi mutum ne mai ilimi. Ya fito daga gidan Fulani Jalligawa. Mutum ne mai sauƙin hali wajen tafikar da rayuwarsa.

A zamanin mulkinsa ya gudanar da sarautarsa cikin sauƙi tare kuma da jama’a. Ya naɗa Musa Ɗan Amadu Bayallige a matsayin Makaman Dutse; wato shugaban rundunar mayaƙan masarautar Dutse. Sai kuma Muhtari Ɗan Abubakar Bagyane a matsayin alƙalin alƙalan Dutse. Sai Kuma Safiyanu Ɗan Ahmadu Gwajabo Bahaɓe (Bahaushe) wanda aka karɓi sarauta a hannun mahaifinsa Sarkin Dutse Ahmadu Gwajabo (1799 – 1807) a matsayin mai kula da al’amuran yau-da-kullum na Masarautar Dutse.

A zamanin mulkinsa ne aka ci Birnin-Kudu da yaƙi. Aka kori sarki Ɗankuri Toro (1819) a matsayin sarkin Haɓawa na ƙarshe a garin Birnin-Kudu.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub