Sarkin Dutse Sambore

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Sambore


Gabatarwa

Sambore shi ne sarkin Dutse na goma. Ba shi da dangantakar jini da sarakunan da suka gaba ce shi. Shi mutum ne mai ƙwazo kuma jarumi. Ya hau gadon sarautar Dutse ne ta hanyar juyin mulki da ya yi wa Yakwabu Kwasau, sakamakon taɓarɓarewar al’amura da kuma jefa jama’a a cikin halin ruɗani da magabacin sarkin ya yi.

Bayan hawansa karagar mulki, Sarki Sambore ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasarsa ta hanyar faɗaɗa ƙasar tasa da kuma ƙara kuɗin harajin gonar dabino da ya yi. A zamaninsa ne ya ci garuruwan Jugurgur, Ma’ai, Fatara, Bukka, Fanisau, da kuma Gurduɓa da yaƙi, suka koma ƙarƙashin mulkinsa. Masarautar Dutse ta ƙara faɗi sannan kuma aka samu ƙarin ƙasar noma mai albarka wanda hakan tabbas ya ƙara haɓɓaka hanyar samar da abinci a wannan yankin.

Sarki Sambore ya mulki Dutse na tsawon shekaru biyar. Ya rasu bayan matsananciyar rashin lafiya da ya yi fama da ita har tsawon shekaru biyu. Matarsa mai suna Maryama, ita ta ci gaba da mulkar jama’a a lokacin da yake fama da wannan rashin lafiya. Ta riƙa karɓar haraji a hannun jama’a sannan kuma ta nisanci yaƙi da sauran maƙwabta.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub