Sarkin Dutse Sulaimanu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Suleman Ɗan Musa 1849 – 1868


Gabatarwa

Sarki Suleman shi ne sarki na talatin da biyu a jerin sarakunan Dutse sannan kuma sarki na huɗu a sarakunan Fulanin Dutse. Shi ɗa ne ga sarkin Dutse Musa Ahmadu (1819 – 1840) kuma jikan sarkin Dutse Amadu Gwajabo (1799 – 1807) ta ɓangaren mahaifiyarsa. Saboda haka shi Bafulatani ne Bayallige.

Bayan rasuwar sarkin Dutse Bello Ɗan Musa (1840 – 1849) wanda yake ƙani ne a gare shi, sai Sarkin Kano Usman Ɗan Dabo (1846 - 1855) ya aikewa da tsohon Sarkin Dutse Musa Ahmadu (1819 – 1840) da yake gudun hijira a Shira cewa ya dawo gida sannan kuma ya faɗi sunan duk wanda yake so ya yi sarauta daga cikin ‘ya’yansa. Saboda haka sai ya miƙa sunan Suleman wanda tare suke gudun hijira a Shira aka naɗa shi a matsayin sabon sarkin Dutse.

A zamanin mulkinsa ya yi fama da yaƙe-yaƙe daga masarautun Haɗejia da ke arewa-maso-gabas da Dutse, da kuma Masarautar Ningi daga kudu-maso-yamma, wanda saboda tsamari da yaƙuƙuwan suka yi da kuma jajircewarsa a fagen yaƙin ake yi masa kirari da Gajere baka da tsoro. Wannan yaƙe-yaƙe da ya yi an riƙa yin su ne ba ƙaƙƙautawa. Ita Ningi a ta nata ɓangaren tana ƙoƙarin sai ta kutsa cikin ƙasar Birnin-Kudu ta maishe ta ƙasarta, ita kuma Haɗejia tana ƙoƙarin cin Miga, Harɓo, da kuma Kiyawa, dukkansu a cikin ƙasar Kano. A zamaninsa ya samu nasarar dakatar da waɗannan hare-hare na Ningi a ƙoƙarinta na kutsawa cikin ƙasar Kano daga ɓangaren Birnin-Kudu da Sumaila. Haka nan ma ya fatattaki sarki Buhari na Haɗeja a ƙoƙarinsa na kutsawa ƙasar Kano ta ɓangaren Miga, Harɓo da kuma Kiyawa.

Haka nan kuma a cikin shekarar 1855, bayan hawan sabon sarkin Kano Abdullahi Ɗan Dabo (1855 – 1882), ya naɗa Sarki Suleman Ɗan Musa a matsayin shugaban rundunar mayaƙan da suka kare ƙasar Kano daga hare-haren waɗancan masarautu guda biyu; Ningi da Haɗeja. A tsawon zamaninsa, sarki Suleman bai samu sukunin zama a gida sosai ba, sakamakon haka sai ya wakilta ƙaninsa Abdulƙadir Ɗan Musa ya riƙa kula da harkokin mulki.

An samu sauyin dangantaka tsakanin Dutse da Haɗeja bayan rasuwar sarkin Haɗeja Buhari a shekarar 1863. Sarkin Dutse Sulemanu shi ya aikawa sabon sarkin Haɗeja Umaru kyautar bayi da dawakai yana yi masa fatan alheri. Wannan ce ma ta saka shi sarkin Haɗeja Umaru samun mafaka a garin Dutse a lokacin da kawunsa ya tsige shi daga kujerar mulki a shekarar 1865.

A cikin shekarar 1868, bayan samun sulhunsu da Haɗeja, ƙasar Ningi ta yi yunƙuri sake kutsawa ƙasar ta Kano dan ta mamaye garuruwan Sumaila da Takai. Saboda wannan dalili sai sarkin Kano Abdullahi Ɗan Dabo (1855 – 1882) ya haɗa rundunar haɗin guiwa wacce ya saka sarkin Dutse Suleman da Madakin Kano na lokacin a matsayin shugabanin wannan ruduna. Dukkansu biyu; sarki Suleman da Madakin Kano a wannan yaƙi aka kashe su. To dama shi sarki Suleman ya bayar da wasiyyar cewa a binne shi filin yaƙi, saboda haka sai aka binne shi a wannan gari na Fajewa inda aka fafata yaƙin. Saboda haka sai ake yi masa laƙabi da Maje Fajewa.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub