Hakimin Dutse Sulaiman II

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Suleman Ɗan Nuhu 1923 – 1960 (Hakimi)


Gabatarwa

Suleman Ɗan Nuhu Bayallige, shi ne Hakimin Dutse na shida, sannan kuma shi ne sarkin Dutse na farko wanda ya samu damar yin karatun zamani. Wannan karatu nasa ya taimaka masa matuƙa wajen samun nasarar kawo sauyi a wannan masarauta ta Dutse. Su ne ɗaliban farko na makarantar ‘ya’yan sarakuna ta Kano, wacce aka fi sani da Makarantar Gidan Ɗan Hausa. Ya halarci wannan makaranta shekarar 1909 shi da wasu ‘ya’yan sarakuna waɗanda daga baya suka riƙe manyan muƙaman sarauta wasu ma sarakunan suka zama. Daga cikin irin waɗannan sarakuna akwai Sarkin Zazzau Malam Ja’afaru Ɗan Isiyaku (1937 - 1959), Malam Bello Kagara, Sarkin Misau Malam Ahmadu, Wazirin Kano Malam Abubakar, Galadiman Kano Malam Abdulƙadir, Malam Abdulwahab daga Haɗeja, da sauransu.

A lokacin da Sarki Bello ya rasu a shekarar 1923, shi Sarki Suleman yana aikin koyarwa a Makarantar Elimantare ta Shahuci da ke Birnin Kano. Zamowarsa jikan Sarkin Dutse Sulemanu Ɗan Musa (1849 – 1868), sai sabon Sarkin Kano Usman Ɗan Abdullahi (1919 - 1926) ya naɗa shi a matsayin sabon Hakimin Dutse a ranar 10 ga watan Agusta na shekarar 1923. Ikonsa ya fi na wanda ya gada, amma dai duk ya taƙaita ne a iya yankin Dutse.

A shekarar 1924, Jami’in Mulki na yankin Dutse Mr. Nor Middleton, ya samu amincewar Rasidan Mr. E.J. Arnnet na cire Kiyawa daga jikin Dutse a kuma yi mata nata Hakimin mai garin digatai ashirin da uku, tare kuma da naɗa Ɗan-Lawan Umar Yola a matsayin Hakimi.

Sarki Suleman Ɗan Nuhu, ya yi amfani da iliminsa wajen sake fasalin Dutse, ta yadda ya kawar da waɗancan matsaloli da ya gada, ya kuma ɗora Dutse a wata sabuwar turba. Saboda wannan namijin ƙoƙari da ya yi, sai Turawa suka yabe shi sannan kuma suka sake ɗora masa wani nauyi na zamowarsa mataimakin Madawakin Kano wanda yana daga cikin manyan ‘yan majalisa a fadar masarautar ta Kano.

Bayan gamsuwa da Turawa suka yi da salon mulkin Sarki Suleman, sai suka sake haɗe yankin Kiyawa, masarautar Dutse ta sake komawa yankin hakimi guda ɗaya a shekarar 1932 a ƙarƙashin mulkin shi Sarki Sulemanu. Wannan kuma ya biyo bayan wata tattaunawa da aka yi a garin Andaza a ƙarƙashin kulawar shi jami’in mulki na yankin Dutse.

Duk da cewa zamaninsa ya ci karo da matsin lambar da Turawa ke fuskanta a faɗin duniya na yunƙurin da wasu yankuna su ke yi na samun ‘yancin kai, Sarki Sulemanu sai da ya yi ƙoƙari ya ɗora Yankin Dutse a tubalin ci gaban zamani wanda ya ci gaba da tofuwa har zuwa yau ɗin nan. Farkon abin da ya fara yi shi ne ganin cewa an samu makarantar Elimantare wacce aka kafa makaranta mai aji biyu a garin Marabisawa a cikin shekarar 1936, wacce daga baya aka canja mata matsugunni zuwa Katangare,  sannan aka ɗaukakata zuwa mai ajujuwa huɗu a cikin shekarar 1945. A shekarar 1949 kuma ya sake samun nasarar kafa wata makarantar a garin Kiyawa. Haka nan a shekarar 1952 aka sake ɗauke waccar makaranta ta Elimantare da ke Katangare aka mayar da ita Garu, matsugunnin da har zuwa yau (2016) a nan take.

A zamaninsa aka riƙa haƙa rijiyoyin kankare. Aka riƙa sabunta rumfunan kasuwa zuwa na zamani, sannan kuma aka samar da hanyar Fuguma zuwa Dutse, da kuma Limawa zuwa Fanisau.

Haka nan ya baiwa Jami’an Mishan na Sudan fili dan gina asibiti a shekarar 1949. Sannan kuma ya yi yunƙuri ya dace Hukumar Gargajiya (Native Authority) ta gina masa Asibitin Jinyar Kuturta a garin Katangare a shekarar 1950 wanda daga baya aka hannanta shi ga su Jami’an Mishan na Sudan suka ci gaba da gudanar da shi. Sannan kuma dai a wannan shekarar aka gina masa Madatsar-Ruwa (Dam) a Magangarar Ruwa ta Kuka wacce ke hanyar Garu zuwa Limawa.

A shekarar 1955, Hukumar Gargajiya (Native Authority) ta gina ɗakin karatu a Fadar Garu wanda ke cike da kayyakin karatun da suka haɗa da littattafai, mujallu, kayan wasanni, radiyon tafi-da-gidanka da sauran kayayyaki dan amfanin jama’a.

Sarki Sulemanu ɗan Nuhu ya rasu a garin Kano, a Asibiti, bayan rashin lafiya da ya samu a shekarar 1960. Kuma an binne shi a gidansa da ke Unguwar Ɗandago, a cikin garin Kano.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub