Sarkin Dutse Tuwai

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Tuwai


Gabatarwa

Tuwai shi ake kallo a matsayin mutumin da ya fara zama sarkin Dutse, ana yi masa laƙabi da mai Asarki Babba saboda hawa kan dutsen Asarki Babba da yake yi dan ganawa da iskokai. Shi mutum ne maharbi, jarumi, ƙaƙƙarfa kuma masanin hulɗa da iskokai. Ya zauna a saman ƙololin duwatsun da ke kewaye da garin Garu. Yakan fita sauran sassa kamar irin su Gaya, Birnin Kudu, Sumaila, da sauransu.

Kamar yadda aka faɗa cewa Tuwai masanin hulɗa da iskokai ne, saboda haka yana yawan yi musu hidima, wanda kuma a duk ƙarshen shekara yakan hau can saman dutsen da ya fi kowane dutse girma wanda ake kiransa da Asarki Babba ya zauna har tsawon mako guda yana hulɗa da aljanu. A irin wannan hawa kan dutsen Asarki Babba da ya ke yi, wata shekara sai iskokan suka umarce shi da ya gina ganuwa ta zagaye garin na garu, sannan kuma ya samar da ƙofa ɗaya tak ta shiga da fita daga garin na Garu wanda kuma ya aikata hakan.

Wata shekara sarki Tuwai ya fita yawon farauta kamar yanda ya saba, sai sarkin Kano na goma sha shida Abdullahi Barja (1438 – 1452 Miladiyya) ya mamayi Dutse ya kuma ci ta da yaƙi. Daga cikin waɗanda aka kama a matsayin bayi har da ‘yar sarki da kuma ‘yar galadima kamar yadda ya zo a Sanusi (2009). Amma a ruwayar Northern Nigerian Publisher (1979), ya zo cewa, da, sarkin ya yi nufin fita zuwa Dutsen da yaƙi, sai Galadimansa mai suna Duwuda ya ce da shi ba sai ya je da kansa ba, shi zai je. Saboda haka Galadima Dawuda shi ya je ya yaƙi Dutse.

Sanusi (2009), ya ce bayan aukuwar wannan yaƙi sai sarki Tuwai ya yi gudun hijira zuwa Birnin Kudu, yana can shi sarkin Kano Abdullahi Barja ya yafe masa kasancewarsa suruki a gareshi. Amma Northern Nigerian Publishing Company (1979), ya ruwaito cewa sai bayan shekara guda da yin wannan yaƙin ne shi sarkin na Kano ya auri ‘yar Sarkin Dutse Tuwai Mai Asarki Babba. Ya yi mulkinsa tsawon shekaru arba’in da ɗaya.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub