Sarkin Dutse Yahai

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Maƙuri Bangon Dutse 1720 – 1732


Gabatarwa

Sarki Yahai shi ne sarkin Dutse na ishirin da huɗu. Sai dai a wata ruyawar ta kunne ya girmi kaka kamar yadda ya zo a (Sanusi, 2009), ta bayyana cewa an ce shi ne Sarkin Dutse na ishirin da bakwai.

Sarki Yahai shi ne sarkin da ya fi kowane sarki shahara daga cikin sarakunan Hausawa. Mutum ne jarumi kuma gwani wajen yaƙi. Ya killace Fadar Masarautar Dutse ta hanyar inganta ganuwar da ta kewaye garin. Ya toshe dukkan hanyoyin da ke kaiwa zuwa ga cikin garin Garu in banda ƙofa ɗaya rak. Daga kan duwatsun da suka kewaye garin Garu ana iya hango nisan mila-milai. Wannan gurin yana da wadatar ruwan da yake gangarowa daga kan dutse da kuma isassun ‘ya’yan itatuwa.

A zamaninsa ya mayar da hankali wajen farautar bayi da samawa masarautarsa kuɗaɗen shiga. A iya tsawon shekaru goma sha biyu da ya yi yana mulki, an ce ya tarawa Masarautar Dutse bayin da yawansu ya kai dubunnai daga sauran garuruwan da ke kewaye da Dutse sannan kuma ya killace su a cikin lokunan duwatsu da ba wanda ke iya sanin inda suke in ba da yardarsa ba. Wannan halayya tasa ta kamen bayi ta saka jama’ar zagayen yankin gudun hijira zuwa Gaya da kuma Birnin Kudu.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub