Sarkin Dutse Yakubu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Yakubu Nabukka 1632 – 1643


Gabatarwa

Sarki Yakubu shi ne sarkin Dutse na goma sha bakwai. Shi jika ne ga sarkin Dutse Yusufu kuma yardajjen ɗan majalisar sarki Mamman Tauroma. Ya rayu a wata ‘yar bukka da ke gidansa na Galamawa wacce daga baya ta zamo fadar mulkinsa ta biyu.

Sarki Yakubu mutum ne mai taka-tsantsan wajen hulɗa da dukiyar jama’a, sannan kuma yana da kunya. A zamaninsa Dutse ta fuskanci hasarar wasu sassa na masarautarta sakamakon hare-hare da ake samu daga Gaya ta ɓangaren yamma da kuma Guddiri ta ɓangaren Gabas. Har lokacin mutuwarsa wasu daga cikin waɗannan yankuna na ƙasa da Dutse ta rasa basu dawowa ba.

Sarki Yakubu ya rasu a shekarar 1643 a cikin bukkarsa da shi da wasu iyalansa sakamakon cutar kwalara.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sarakunan Dutse

Haɓawa

Fulani


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub