Sarkin Dutse Yakwabu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Yakwabu


Gabatarwa

Yakwabu Kwasau shi ne sarkin Dutse na tara. Sarki Yakwabu Kwasau jika ne ga sarkin Dutse Amadu Maranje, sannan kuma ƙanin sarki Labun Mai Achiza ta ɓangaren mahaifiya. Sarki Yakwabu ya kasance mutum ne mai yawan buri wanda hakan ta sanya shi faɗaɗa Fadar Masarautar Dutse inda ya mai da ita ta koma yamma da asalin dutsen Gadawur, sannan kuma ya fitar da wata ƙofar da ta ke kallon Unguwar Bayi wacce aka saka wa suna Ƙofar Bai. Wannan dalili na yawan buri nasa ya saka ake kiransa da suna Kwasau.

A lokacinsa sai da baitil-malin masarautar ya durƙushe saboda yawan buƙatu da yake yi. Ya sallami wasu daga cikin mashawartansa ya kuma tarwatsa masu jayayya da wannan halin nasa. Wannan kuma ta haifar da ruɗanin da ya kai ga sanadiyyar barinsa kujerar mulki a shekarar 1554 ya kuma ƙaura shi da iyalansa zuwa Gwari.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub