Sarkin Dutse Yasufu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Yusufu Atakalafiya 1609 – 1616


Gabatarwa

Sarki Yusufu shi ne sarkin Dutse na goma sha biyar. Shi ne shugaban rundunar mayaƙan Dutse (sarkin yaƙi) a zamanin Sarki Jarmai Babba. Sarki Yusufu bashi da wata dangantaka ta jini da sarakunan da suka gaba ce. Kafin zamowarsa sarki a garin Takalafiya yake zaune. Mahaifansa kuma mutanen Zai ne.

Wannan suna na Takalafiya kuwa ya samo asali ne saboda samuwar kunamu da macizai a ƙarƙashin duwatsun da ke kan hanyar zuwa gidansa.

Sarki Yusufu shugaba ne na jama’a, mutum ne mai son sulhu. Garuruwa da dama sun mara masa baya a yunƙurinsa na haɓɓaka tattalin arziƙin Masarautar Dutse. Sarki Yusufu mutum ne mai tsantseni game da dukiyar jama’a.

Wasu mutanen da ba a san ko su waye ba, su suka kashe shi ta hanyar kisan gilla a shekarar 1616. Bayan rasuwarsa iyalansa sun ci gaba da rayuwa a wancan gida nasa da ke Takalafiya. Haka nan kuma gidan ya ci gaba da wanzuwa har lokacin da sarki Sulaimanu II (1923 – 1960) ya mayar da gurin maƙabarta bisa umarnin Turawa dan hana jama’a binne/bisne gawarwaki a gidajensu saboda dalilan kiwon lafiya.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sarakunan Dutse

Haɓawa

Fulani


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub