Sarkin Dutse Zubairu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Dutse Zubairu Tsohon Mutum 1737 – 1797


Gabatarwa

Sarki Zubairu Tsohon Mutum shi ne sarki na ishirin da shida a jerin sarakunan Dutse. Sarki Zubairu jarumi ne shi, ya ƙware sosai wajen sanin makamar yaƙi a zamanin sarkin Dutse Maƙuri (1720 – 1732). Ya gudu zuwa Birnin-Kudu a zamanin yaƙinsu da sarki Ada (1732- 1735). Shi ne ya cike giɓin da sarkin Dutse Ada ya bari.

Babbar gudunmawar da ya bayar ita ce ta sake zagaye birnin Dutse da ƙarin ganuwar da aka yi ta da kwaɓaɓɓiyar ƙasa da kuma duwatsu. Wannan aiki da ya yi ya ƙara samar da wadatuwar abinci ga garin Garu da sauran garuruwan da suka shiga cikin wannan sabuwar ganuwa tasa. Samuwar wannan ganuwa ta biyu ita ta ƙara yawan ƙofofi goma sha ɗaya. Wannan sabuwar ganuwa riɓi ce a kan wacce sarki Tuwai (1421 – 1463) ya samar tun da farko bisa umarnin iskokansa.

Sarki Zubairu Tsohon Mutum ya yi ritaya sakamakon wata ‘yar musgunawa da aka yiwa matarsa mai suna ‘yar’gyatuma. Ya mulki wannan masarauta ta Dutse har tsawon shekaru sittin.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub