Waƙar Hafiz Koza; Kamar Kumbo, Kamar Katanta

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Waƙar Hafiz Koza Ga Sarakunan Kano; Marigayi Alhaji Ado Bayero, CFR da Muhammadu Sanusi II, CFR


KAMAR KUMBO, KAMAR KATANTA

Allahu Sarki, Rabbu wanda ya yo sama,
Ba tokara ko tanƙwara ga samaniya.

Shi ne ya tsara ƙashi da tsokar Ɗan'adam,
Shi yai jinin da yake gudana jijiya.

In lokacin mutuwa ta zo ba tantama,
Duk sai a bar komai a riski Gwani ɗaya.

Dangi a ranar sai zaman yin tuntuni,
Tuna ayyukan da ka yo a faɗin duniya.

In ka yi hairi sai a rinƙa yaba maka,
Sharrin a bar ka da shi cikin ƙabari, ji ya!

Duk wanda yai hairi a nan sai an faɗi,
Ko ba shi nan, har nan da tashin duniya.

Wannan ta sa na tuna da Sarki adali,
Sarkin Kano Ado masoyin gaskiya.

Duk wanda ke yin rayuwa ya san haka,
Ilmi abin so ne ga ɗa na halaliya.

Sarkin Kano Ado Mu'allimu shi yake,
Ya tattare ilimai wurinsa gaba ɗaya.

Ilmi na Addini haɗa har zamani,
Ya yi su, ya kuma ce a je a yi bai ɗaya.

Kuma in batun aiki na gwamnati ma ake,
Manyan muƙamai ya riƙa shi tun jiya.

Yai ayyukan mulki yana ɗan ƙanƙane,
Kafin ya zo gadon gida ba tankiya.

Aiki na banki ya yi ba mai yin musu,
Yai Jami'i na tsaron Kano baki ɗaya.

Babban muƙami, ya riƙe N. A. Kano,
Har ma Jakadanci ya je Singaliya.

Ya zam wakilin majjalissa tun a da,
Na Arewaci, kuma ya tsaya kan gaskiya.

Ɗan kasuwa na cikin gida har ƙetare,
Kuma ya yi noman cimaka ta halaliya.

In yo batun mulkin gida da ya yo riƙo,
A gidan 'Fulani', Kano nake son waiwaya.

Ya hau Sarauta tun yana ɗan shekaru,
Thirty three, ya riƙe Kano baki ɗaya.

Ba nuna bambanci; talakka da mai akwai,
Mai Martaba shi ba shi son mai wariya.

Mulkinsa yai har shekaru hamsin plus,
Kuma ya yi har ya gama shi lami-lafiya.

Sai addu'ar rahama gare shi ta dauwama,
Allah haɗa shi da Ɗaha Khairul Anbiya.

Bayan wafatin San Kano Ɗan Bayero,
Sarki Sanusi na biyyu ne ke yin biya.

Shi Malami ne mai riƙon Sunnah gagam,
Burinsa kullum ɗaukakar Islamiya.

Ko Juma'ar farko da samun Martaba,
Huɗubar da yai tamkar a Saudi-Arebiya.

Kuma in ana magana ta ƙaunar al'umma,
Wannan kwa ba a Kano ba, duk Nijeriya.

Mai tausayawa ne ga dukkan talikai,
Ku tuno abinda ya afku kan ɗan Zariya.

Ya je biya wa mahardacin nan ne kuɗin,
Aikin da za a fitar da shi can Indiya.

Ya haɗa da wannan taliki ɗan Zariya,
Miliyan plus miliyan, abun sai godiya.

A cikin jimillar shekaru ukkun da yai,
Hairinsa ya nashe dukan Nijeriya.

Lallai abun a yaba, yabo kuma mai yawa,
Sai dai mu yo fata ta ƙarin lafiya.

Ya daɗe bisan karaga ana damu da shi,
Har mu na nesa mu riski alfarmarsa ya.

Ba mai nufin sharri ba ne Sarkin Kano,
A fahimci alƙiblarsa ta nufi gaskiya.

In yai batu a tsaya a saurara da kyau,
Aya, Hadisi ce idan an bibiya.

Duk masu surutu a kan Mai Martaba,
To hassada ce ɗai da ƙin a bi gaskiya.

Sun so su sam dama a ba su ƙasar Kano,
Mulki a ba su, su hau a don su yi danniya.

An gane kura dai akwai yin handama,
Shi kau dila an san shi sai wayon tsiya.

Ni nai kira a gare ku al'ummar Kano,
Ku riƙe shi Sarkin naku kar ku yi tankiya.

Allah ya ja kwanansa har mu ci gajiya,
Fatar da zan yi ya mulki kaf Nijeriya.

Nan zan tsaya Hafiz na Koza ku ce da ni,
A cikin masoya na zamo ƙwallin ɗaya.

Mai Martaba Sarkin Kano ga addu'a,
Allah ya sa ka ga Ɗaha tun nan duniya!


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub