Hausa Baƙar Magana

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hausa Baƙar Magana


Gabatarwa

Baƙar magana, magana ce wacce idan aka gayawa mutum za ta harzuƙa shi ta ɓata masa rai. Zarruƙ, Kafin Hausa, da Alhassan (1987), suka ce: “Baƙar magana ita ce duk wata magana da aka yi domin ta sosa zuciyar wani mutum”.

Sigogin Baƙar Magana

Akwai sigogi da dama da ake bi wajen yin baƙar magana, daga ciki akwai:
  1. Baƙar Magana Kai Tsaye: Ita ce dukkan wata magana da ake fitowa fili a gaya wa mutum domin ransa ya yi baƙi. Misali, na cinye idan an isa a ƙwata da ƙarfi. Wannan magana ce da ake gayawa wanda ake ganin an fi ƙarfinsa. Dole wannan magana ta ɓatawa wanda aka gayawa rai, saboda yana kallo ga haƙƙinsa a hannun wani, amma kuma an ce idan ya isa ya ƙwata da ƙarfi idan kuma ba haka ba, to an ciye masa.
  2. Baƙar Magana ta Hanyar Gatse: Baƙar magana ce da ake yinta a fakaice. A irin salo na wannan baƙar magana akan yi amfani da gatse ne; wato halin da ake faɗin kishiyar abin da ake nufi. Misali, mutum ne ya je kasuwa zai sayi wani kaya, sai mai kaya ya zuga wa kayan kuɗi, to a nan mai saye zai iya gaya wa mai sayarwa baƙar magana a fakaice. Kamar a ce ya kamata a sayar da kayan Naira dubu, sai shi mai kayan ya ce a saya Naira dubu uku, to a nan mai saye zai iya gayawa mai sayar da kayan baƙar mata ta cikin gatse kamar ya ce, a’a, naira dubu goma.
  3. Baƙar Magana Cikin Raha: Baƙar magana ce da akan yi ta domin nishaɗi ba domin neman faɗa ba. Yawanci mahauta su suka fi yin wannan. Misali, idan aka samu mahauci yana gasa nama, ana iya tambayarsa a ce da shi, naman ya gasu kuwa? Shi kuma zai iya amsawa da cewa, yanzu na ke fiɗa. Wato kenan ba a gama feɗe dabbar bama tukuna bare a yi maganar gyara naman a saka shi jikin tsinke. Ko kuma ta wata hanyar mutum mai yawan shekaru ya rage shekarunsa, ana iya gaya masa magana ta cikin raha a ce da shi, a’a, gobe za a raɗa maka suna. Wato kenan shi jariri ne.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Junaidu I. da “yar’Aduwa T.M. (2002). Harshe da Adabin Hausa a Kammale Don Manyan Makarantun Sakandare. Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan - Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub