Bayajidda

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Bayajidda


Gabatarwa

Bayajidda, wani jigo ne a tarihin yaɗuwar sarauta a ƙasar Hausa. Asalin wannan mutum ya zo ne daga ƙasar Bagadaza, wacce a yanzu aka fi saninta da Ƙasar Iraƙi. Shi ɗan’uwa ne ga sarkin Bagadaza na wancan lokacin. Cikakken sunansa kuma shi ne Abu Yazid.

Bayajidda, ya baro ƙasar Bagadaza tare da wasu mutanensa, a bisa dalilin saɓani da suka samu tsakaninsa da masu sarautar garin.

Ya fara yada zango a ƙasar Barno bayan doguwar tafiyar da ya yi, wadda ya ratsa ƙasashen Masar (Egypt) da Sudan kafin isowarsa ƙasar Barno inda ya fara yada zango.

Lokacin da Bayajidda ya iso ƙasar Barno, ya iso da runduna mai ƙarfi wadda sarkin Barno na zamanin ya kalleta a matsayin barazana ga mulkinsa. Saboda wannan dalili sarki ya fara tunanin yadda zai yi ta cikin dabara ya zama ya mallake jama’ar Bayajidda daga baya kuma ya sallame shi daga garin. Wannan tunani na sarkin Barno ya haifar da aurar da ‘yarsa mai suna Magira ga shi Bayajidda.

Faruwar wannan aure tsakanin Bayajidda da wannan ‘ya ta sarkin Barno ta haifar da kyakkyawar dangantaka tsakaninsu, wadda har ta kai ga shi Bayajidda yakan haɗa rundunarsa da ta sarkin Barno su je yaƙi domin kare daular ta Barno a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso. Ƙulluwar wannan dangataka kuma ta bai wa sarkin Barno damar mallake wasu daga cikin jama’ar Bayajidda, abin da ya haifar da fuskantar barazana ga rayuwar Bayajidda abin da ya jawo sulalewarsa daga daular Barno.

Ya baro garin Barno shi da matarsa ya nufo Yamma, bai zame ko’ina ba sai wani gari da ake cewa Garun Gabas, wanda yanzu garin yana ƙarƙashin mulkin masarautar Haɗeja. A wannan gari wasu maruwaitan suka ce ya bar matar tasa da ciki ta haifi ɗa namiji, wasu kuma suka ce suna nan tare ta haifi ɗan. Koma dai yaya ne, duk sun yarda a kan cewa ta haifi ɗa namiji.

A wannan gari ma dai Bayajidda hankalinsa bai kwanta ba, saboda yana ganin kamar za a iya biyo shi daga Barno, saboda haka sai ya ƙara tafiya Yamma inda ya sake yada zango a garin Gaya. Bayan ya zauna a wannan gari na Gaya, sai kuma ya yi nufin tashi don ƙara wa gaba. Abubakar (2007), ya ce sai suka bashi takobi da wuƙa.


Takobi da Wuƙar Bayajidda

Da wannan takobi da wuƙa ya sake nausawa Arewa har sai da ya iso garin Daura. Ya shiga wannan gari na Daura ta Ƙofar Gabas. Waɗannan takobi da wuƙa da aka bashi, da su ya yi amfani ya kashe wata macijiya da ke addabar jama’a, ta ke hana su ɗiban ruwa a rijiyar Kusugu.

Ganin irin wannan bajimta da Bayajidda ya yi, kamar yadda ya zo a (Abubakar, 2007), sai Magajiya (sarauniya) ta wannan zamani ta saka shi cikin sarauta inda kuma daga baya ta aure shi sannan kuma ta ƙara masa da kuyangi.

Bayajidda ya haifi ‘ya’ya biyu, ɗaya ɗan sarauniya, ɗaya kuma ɗan kuyanga. Shi ɗan kuyangar shi ake kira Karab-da-Gari (Karɓe-Gari), shi kuma ɗan sarauniyar sunansa Bawo.

Bayan rasuwar Sarauniya da shi Bayajidda, sai ɗansu, wato Bawo ya gaji sarautar Daura. Wannan kuma shi ne abin da ya sauya al’adar Daura ta yin sarautar mace ta koma hannun namiji.

Suma waɗannan ‘ya’ya na Bayajidda daga baya sun hayayyafa, shi Bawo yana da ‘ya’ya da suka zama sarakunan Hausa Bakwai waɗanda suka haɗa da, Gazauru wanda ya sarauci garin Daura, sai kuma Gunguma wanda ya mulki Zazzau, sai kuma Bagauda wanda ya mulki Kano, sai kuma Duma wanda ya sarauci Gobir, sai Kumayau wanda ya sarauci Katsina, sai kuma Zauna-Kogi wanda ya mulki Rano. Waɗannan garuruwa da aka ambata, wato, Daura, Kano, Zazzau, Katsina, Gobir, Garun Gabas da Rano, su ake kira Hausa Bakwai.

Sai kuma shima Karab-da-Gari yana da nasa ‘ya’yan, su kuma, su suka sarauci ƙasashen da ake kira Banza-Bakwai waɗanda suka haɗa da, Kebbi, Yawuri, Zamfara, Ilorin, Nupe, Ƙasar Gwari, da Kwararrafa.

Wannan shi ne Bayajidda wanda ake kira da Abu yazid.

Darrusa

Akwai ka-ce-na-ce da kuma cece-ku-ce game da wannan tarihi na Bayajidda. Wasu daga cikin masana suna kiransa da tastuniya, wasu kuma suna ganin cewa hakan ta faru. To, abu ne mai yiwuwa hakan ta faru. Saboda dama shi mutum haka Allah ya halicce shi mai yawo ne daga guri zuwa guri. Idan da za mu kalli haɓakar garin Makka da kafuwar wasu garuru a zamanin Jahadi Shehu Ɗanfodiyekamar kafuwar ita kanta Sakkwaton da ma wasu garuruwa da zuwan Bature Najeriya ne ya sa aka kafa su kamar Kaduna, Lagos da sauransu za mu iya gaskata wannan labari.

Sannan kuma abu na biyu; Marigayi Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya da sauran abokan rubutunsa sun aje wannan labari a matsayin tarihihi; wato labarin da tsawon lokaci ya saka tantance gaskiya da ƙarya a cikinsa za ta wuyata.

Babban abin da ya haifar da wannan ruxani kuwa shi ne danganta Bayajiddan da asalin Hausa wadda kuma a maganar gaskiya ita ce babu. Ai zahirance za mu ji cewa duk garuruwan da ya yada zango a cikin su mutane ya taras a garuruwan Ka ga kenan ya zo ya taras da wasu. Abin sani dai kawai shi ne zuwansa ne ya bunƙasa harkar sarauta a ƙasar Hausa.

Manazarta:


Abubakar M.S. (2007). Taƙaitaccen Tarihin Daura. Majalisar Sarkin Daura. An buga a: Ammani Printing Press.

Tattaunawa da Wakilin Tarihin na Daura da kuma Dogarin Sarkin Daura mai suna Ɗandaushe, a ranar 24 ga watan Mayu na shekarar 2016.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub