Tsarin Sauti: Furucin Wasali

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tsarin Sauti: Furucin Wasali


Gabatarwa

A Daidaitacciyar Hausa kuma a fagen nazarin sauti, akwai wasula guda goma sha biyu a bisa haɗuwar Zarruƙ, Kafin Hauda da Alhassa (2010), da kuma Yahaya, Zariya, Gusau da ‘Yar’aduwa (2006). Sani (2007), kuma ya saɓa da su ya ce guda goma sha uku ne.

Goma daga cikin su ana kiransu gwauraye ko tilo. Waɗannan gwaurayen wasula kuma an sake karkasa su zuwa dogaye da gajeru. Sauran guda uku kuma ana kiran su masu aure ko masu goyo.

Ma’anar Wasali

A fagen nazarin sauti, wasali shi ne harafin da lokacin da ake furta shi gaɓoɓin furuci basa taɓa ko kusantar juna, sannan kuma iska bata samun tangarɗa.

Dukkanin ƙwayoyin sautin wasali guda goma sha uku masu ziza ne. Sani (2007) ya ce: “Dukkan wasula masu ziza ne, ba kamar takwarorinsu baƙaƙe ba, inda yake wasu masu ziza ne, wasu kuma marasa ziza wasu kuma ‘yan ba ruwanmu”.

Nazarin Furucin Wasali

Ana nazartar furucin wasalin Hausa ta hanyar la’akari da abubuwa biyu: tsayi da kuma siga.

Tsayin Wasali

Abin da ake nufi da tsayin wasali a nan shi ne lokacin da ake ɗauka wajen furta wasali, cewa, ana jan lokaci wajen furta shi ko kuwa ba a ja? Waɗanda ake jan lokaci wajen furta su, su ne dogaye. Gajeru kuma ba a tsawaita sauti wajen furta su. kuma duka yawansu ɗaya ne; wato biyar-biyar ne.

Dogayen Wasula

Dogayen wassula su ne: /aa/, /ee/, /ii/, /oo/ da kuma /uu/.

Gajerun Wasula su ne: /a/, /e/, /i/, /o/ da kuma /u/.

Amma a wajen rubutu duka ɗaya ne babu bambanci.

Babban muhimmanci ko amfani da suke da shi, shi ne cewa, ta hanyar su ne kaɗai ake iya gane ma’anar kalma a cikin zance. Misali:

  1. Faɗa da ma’ana ta husuma, kamar ka ce suna faɗa.

Faɗaa da ma’ana ta magana. Kamar ka ce jiya ya faɗa a gabana.
Faaɗaa da ma’ana ta shiga. Kamar ka ce ya faɗa ramin.

Idan muka lura babu bambanci wajen rubuta kalmomin kamar yadda suka zo a cikin jimla. Amma furuci ya bambanta mana su.

  1. Turi, da ma’ana ta rini. Kamar ka ce Ado yana turin kaya.

Tuurii, da ma’ana ta hankaɗa ko tunkuɗa abu. Kamar ka ce suna turin mota.

  1. Jakaa, da ma’ana ta mazubi. Kamar ka ce zuba a cikin jaka.

Jaakaa, da ma’ana ta dabba. Kamar ka ce ga jaka can.

Sigar Wasali

Sigar walasi a fagen nazarin furucin wasali ita ce siffar wasali. A nan ana la’akari da abubuwa biyu wajen gane sigar wasali: Leɓɓa da kuma harshe.

Matsayin Leɓɓa

A nan, ana duba yanayin da leɓe yake a yayin furta wasali. Leɓɓa a nan sukan nuna halaye guda biyu:

Zumɓurarru/Kewayayyu

Waɗannan su ne wassulan  idan aka zo furta su laɓɓa sukan kewaye ko su zumɓura. Wasalin /o/ da /u/, su ne a wannan rukuni.

Marasa Kewaya/Shatattu

Waɗannan su ne wassulan da idan aka zo furta su leɓɓa suke bajewa. Wassulan su ne /a/, /i/ da /e/.

Dangane da matsyain leɓe a wajen furta gwaurayen wassula babu bambanci.

Matsayin Harshe

Ana lura da abubuwa biyu dangane da matsayin harshe a furucin wassula: Ana lura da sashe ko ɓangaren harshe wajen ɗagawarsa a lokacin furuci, cewa gabansa ne ya ɗaga, ko tsakiyarsa ko bayansa? Sannan kuma wannan ɗagawar da ya yi ina ne muhallinsa? Ya ɗaga sama ne, ko tsakiya ko kuwa kwanciya ya yi?

Ɗagawar Harshe

Dangane da ɗagawar harshe, wassula sun rabu gida uku:

  1. Wasulan Gaban harshe: Su ne wasulan da gaban harshe yake ɗagawa a yayin furta su. A nan akwai: /i/ da /e/.
  2. Wasulan bayan harshe: Su ne wasulan da idan aka zo furta su bayan harshe yake ɗagawa. Wasulan su ne: /u/ da /o/.
  3. Wasalin tsakiya: Shi ne wasalin da idan aka zo furta shi tsakiyar harshe tafi ɗagawa. Wasali ɗaya ne wanda kuma shi ne /a/.

Muhallin Harshe

Muhallin harshe a nan na nufin bigire ko gurin da harshe ya tsaya a cikin baki yayin da ya ɗaga domin furta wasali. Yana da muhallai guda uku kamar haka:

  1. Sama: Saboda ɗagawarsa saman harshe domin furta su. Sashen harshen da ya ɗaga har yakan taɓa saman baki, wasulan /i/ da /u/, su ne  a nan gidan.
  2. Tsakiya: /e/ da /o/, su ne wasulan da sassan harshen da suke ɗagawa  domin furta su suke tsayawa a tsakiya.
  3. Ƙasa: /a/, shi ne wasalin da sashen harshe da yake furta shi, yake kwanciya a ƙasan baki ya lafe.

Furucin Wasula Masu Aure

/au/, /ai/ da /ui/. Sukan zo a cikin:

  1. /au/: Ɗauri, lauje, jauje, Saude, daure da sauransu.
  2. /ai/: Daidai, sai, rai, kai, mai, da sauransu.
  3. /ui/: Tukuici, lunkui da sauransu.

Furuci

Yanayin furucin wasula masu aure ya bambanta dana gwauraye, saboda ana furuci biyu ne a lokaci guda.

  1. /au/: dangane da abin da ya shafi furucin wannan wasali, za a fara furta /a/, ta hanyar shimfiɗa harshe a ƙasan baki, sannan a ɗaga shi sama tare da jansa baya, domin a furta /u/.
  2. /ai/: Za a fara furta /a/, ta hanyar shimfiɗa harshe a ƙasan baki, sannan a yi sama da shi a turo shi gaba domin a furta /i/.
  3. /ui/: Za a fara furta /u/, ta hanyar ɗaga bayan harshe zuwa sama, sannan a turo shi gaba a furta /i/.

Idan muka taƙaita a nan, za mu ga cewa, wasulan Hausa guda goma sha uku ne a fagen furuci; wato fannin nazarin sauti. Goma daga cikin waɗannan wasula gwauraye ne ko kuma tilo, uku kuma an kiransu masu aure ko kuma tagwai. Gwaurayen nan sun kasu zuwa dogaye da kuma gajeru guda biyar-biyar daidai-wa-daida.

Wajen furta gwaurayen wasula ana lura da tsayinsu da kuma muhallin harshe. Tsayin a nan shi ne tazarar lokacin da ake ɗauka wajen furta su. Muhallin harshe kuma ana lura da sashen da ya ɗaga ko ya kwanta da kuma muhallin da yake a lokacin furucin wanda ka iya zama sama, tsakiya ko kuma ƙasan baki.

Masu aure ko kuma tagwai, ana lura da furucin ɗaiɗaikun wasulla da suka yi auren ne kuma a tare.

Manazarta:


Junaidu I. da ‘Yar’aduwa T.M (Babu Shekara). Harshe da Adabin Hausa a Kammale Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Nigeria.

Sani M.A.Z. (2007). Tsarin Sauti Da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Sani M.A.Z., Muhammad A. Da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Langugae Don Masu Rubuta Jarabawar WASC da SSCE. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M da ‘Yar’aduwa T.M. (2006). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub