Hausa Hawan Daba

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hawan Daba


Gabatarwa

Bikin Hawan Daba sabon biki ne a Ƙasar Hausa. Sabon biki a nan yana nufin ba biki ne na tun dauri ba, wanda Bahaushe ya gada tun kaka-da-kakanni, biki ne da ya shigo Ƙasara Hausa bayan zuwan Turawa.

Ana bikin Hawan Daba ne don sada muzunci tsakanin sarakuna ko kuma tarbar wani babban baƙo.

A wannan biki na Daba sarakuna kan haɗu da su da hakimansu kowane ɗaya da tawagarsa su hau dawakai. Za su yi ado iya ado, haka nan ma dawakan nasu za a caɓa musu ado.

Ana gudanar da wannan biki na Daba a filin da yake da faɗi sosai. Waɗancan tawagogi na sarakuna waɗanda suke mahaya dawakai, za su riƙa zuwa suna kewayowa sannan su zo gaban babban sarki su kawo caffa ko kuma shi babban baƙon da ake karramawa da wannan biki na Hawan Daba.

Wannan biki na Hawan Daba wata hanya ce ta ƙulla zumunci tsakanin sarakuna da kuma nuna wa baƙon da ake karramawa daɗaɗɗiyar al’adar da Bahaushe yake da ita.

An gudanar da hawan daba na farko a arewacin Najeriya a cikin shekarar 1975 a garin Kaduna domin karrama sarauniyar Ingila.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Darrusan Hausa

  • Darrusan Hausa

  • Bukukuwa


    Wasanni



    Ƙasar Hausa



    Musulunci


    Zuwan Turawa


    Tarbiyya


    Kayan Kiɗan Hausa


    Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


    Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



    Sauran Shafukanmu:

    Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub