Hikaya

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hikaya


Gabatarwa

Hikaya labari ne da ya shafi wasu mala’iku, da waliyyai. Hikaya a wasu lokutan kuma takan zama ƙagaggen labarin da abin da ke cikinsa zai iya faruwa, ko kuma labarin wani abin mamaki da ya faru da wani mutum.

Hikaya ta bambanta da ƙissa saboda ita ƙissa annabawa zalla ta shafa. Sannan kuma ta bambanta da almara (labarin da aka ƙaga kenan), saboda abin da labarin ke ɗauke da shi zai iya faruwa ko kuma ma ya riga ya faru.

Ana gina labarun hikaya a kan mutane, iskokai, rauhanai, dabbobi, tsuntsaye, da sauran halittu.
Labarun hikaya cike suke da nishaɗi, da kuma darrusan da suka shafi rayuwa, a wasu lokutan sukan zamo gargaɗi saboda zuwan irin labarin nan na gani-ga-wane, ya ishi wane tsaoron Allah a cikinsu.

Hikayar Kunkuru da Gauraki

Wai wata rana, wasu gauraki guda biyu, za su yi bulaguro, sai wani kunkuru abokinsu, ya roƙe su su tafi da shi. Suka ce, “To, kai ga shi ba ka da fuffuke. Yaya za mu iya tafiya tare?” Ya nace shi sai dai sun tafi da shi. Don haka sai suka yi dabara, suka ɗauko wata sanda, kowace tsuntsuwa ta kama gefen sandar guda, shi kuma kunkuru ya riƙe sandar da bakinsa, suka tashi da shi. suna cikin tafiya a sama, sai suka zo wucewa ta kan wani gari, sai suka ga wani abin dariya na aukuwa a garin. Sai ɗaya gaurakiyar ta ce “La, kin ga wani abin dariya, zomo na korar akuya”. Ko da ‘yar uwar ta duba ta ga haka, sai ta ƙyalƙyale da dariya. Da kunkuru ya ji suna dariya, sai ya buɗa baki wai zai tambaye su abin da ya sa suke dariya. buɗe bakinsa ke da wuya, sai ya suɓuto ƙasa, ya faɗo, ya farfashe. (Wai shi ya sa ake ganin bayan kunkuru duk a tsattsage). To, kun ga kunkuru bai iya bakinsa ba kenan.

An ciro wannan hikaya daga littafin Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausa, na Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo, Jami’ar Bayero, Kano.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’, Gidan Sa’adu Zungur, Kano – Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub