Hikayoyi

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hikaya: Amana Taskar Arziƙi

Gabatarwa

Wata rana wani yaro yana tafiya makaranta, sai ya tsaya a wani kanti dan sayen abin rubutu, bayan ya saya ya biya, kafin ya bar gurin sai wani mutum ya zo, shi ma ya yi tasa sayayyar. Da mutumin nan ya fito da jakar kuɗinsa ya biya kuɗin kayayyakin da ya saya, a ƙoƙarinsa na mayar da wannan jaka tasa aljihu, sai jakar ta faɗi ƙasa bai sani ba. Yaron nan yana waigowa, sai ya ga jakar nan. Sai yaron nan ya ɗauki jakar nan cikin hanzari ya bi mutumin nan da gudu, ya damƙa masa abar sa.

Cikin mamaki mutumin nan ya kalli wannan yaro ya ce da shi, yaro, Allah ya yi maka albarka. Yaro ya amsa, ya ce Amin. Sai mutumin nan ya ɗauko kuɗi ya baiwa yaron nan, shi kuma ya ƙi karɓa. Sai mamaki ya sake kama mutumin nan, sai ya tambayi yaron sunansa, makarantarsu, da kuma ajin da ya ke. Duka yaro ya gaya masa.

Bayan shekara biyu da faruwar wannan lamari, sai ga wannan mutum a wannam makaranta ɗauke da takardar shedar aiki ya kawo wa wannan yaro, ya ɗauke shi aiki a kamfaninsa. Ashe dama mutumin nan ya riga ya lissafa shekarun da wannan yaro zai gama karatun sa a wannan makaranta. Saboda gasuwar da ya yi cewa, lallai yaron nan zai iya riqe masa amana.


Ana iya turo labari domin a wallafawa ta:
Was-af: 0803 964 8244 (+234803 964 8244)
Imel: rumbunilimi@gmail.com


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub