Ƙa’idojin Rubutu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙa'idojin Rubutu


Gabatarwa

Ƙa’ida, ita ce doka, wacce duk wanda ya saɓa, to ya kauce hanya. Hausa, a matsayinta na babban Harshe daga cikin manyan harsuna a duniya, ta kasu zuwa Hausar Baka da kuma Hausar Rubutu.

Hausar baka, ita ce wacce ake magana da ita, wacce kuma take da kare-kare masu yawa. Jigajigan cikin kare-karen su ne waɗanda ake amfani da su a manya kuma daɗaɗɗun masarautun Hausa da suka haɗa da Kano, Gobir, Daura, Zazzau, Katsina sannan kuma daga baya Sakkwato da sauransu.

Ita kuwa rubutacciyar Hausa, ita ce Hausar da ake rubuta dukkan wani rubutaccen abu a cikin Harshen Hausa. Ita ce Hausar da take da ƙa’idojin rubutun Hausa. Samuwar wannan ƙa’idoji na rubuta Hausa a bokonce, shi ne ya samar da Daidaitacciyar Hausa. Waɗannan ƙa’idoji da ake kiyayewa su ke mayar da rubutu ya zama ya isar da cikakken saƙon da ake son ya isar. Shi ke saka rubutu ya zamo mai daɗin  kallo da kuma karantawa da sauransu. A wannan rubutun da mai karatu yake karanta za mu duba waɗannan ƙa’idojin:

  1. Ƙa'idojin raba kalma
  2. Ƙa'idojin haɗe kalma
  3. Nuna mallaka
  4. Manya da Ƙananan Baƙaƙe
  5. Alamomin rubutu

Manazarta:

Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa (Yadda Yake Da Yadda Ake Yinsa) Don Masu

Koyo da Koyarwa. Ibrash Islamic Publications Centre L.T.D., 31 Adelabu Street, Surulere, Lagos-Nigeria.
Jinju M.H. (2007). Rayayyen Nahawun Hausa. Northern Nigerian Publishing Company L.T.D., Gaskiya Building, Zaria, Kaduna-Nigeria.

Sani M.A.Z, Muhammad A. da Rabeh B. (2000). Exams Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC,
Ibadan – Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M. (2007). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan – Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Uku.
University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub