Kuntukuru

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kuntukuru


Gabatarwa

Kuntukuru abin kiɗa ne wanda ya ke a matsayin mataimaki a cikin kayan kiɗan kalangu. Shi ma ganga ce mai zaman kanta wacce ke da guloli guda biyu. Sai dai, ba a kaɗa shi, shi kaɗai sai an haɗa shi da kalangu.

Kayan Haɗin Kalangu

  1. Icen Ƙirya ko Alulluba
  2. Fatar akuya ko ɗan tayin akuya
  3. Tsirkiya: Jemammiyar fata ce da ake yayyanka ta ana yin igiya da ita. da ita ake ɗame kalangu ana rufe shi.
  4. Saƙe: Saƙaƙƙen zare ne da masaƙa ke saƙawa. Da shi ake yin maratayi.


Kuntukuru

Manazarta:


Gusau S.M. (2017). Kayan Kiɗan Hausa. Centuary Research and Publications, Kano – Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan – Nigeria.  

Tattaunawa da Umaru mai gurmi a garin Uke ta jahar Nassarawa a ranar Alhamis 14/3/2018.

Tattaunawa da Sarkin Kiɗan garin Alitini, Isma'ila Namarke, a garin Alitini, ƙaramar hukumar Warawa, a Jahar Kano, Najeriya. A ranar 17 ga watan 6, na shekarar 2017.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub