Magani a Ƙasar Hausa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Magani a Ƙasar Hausa


Gabatarwa

Akwai hanyoyi masu yawa da Bahaushe ya ke bi wajen magance duk wata cuta da ta same shi. Haka nan wannan fage na magani na daga cikin fagagen da ke nuna ɗimbin hikimomi da Allah ya yiwa Bahushe. A gargajiyance kuma a al’adance, Bahaushe yana yin maganita hanyoyin da dama.


Maganin Gargajiya a Kasuwa

Magani ta Hanyar Itatuwa da Ciyayi

Amfani da itatuwa da ciyayi daɗaɗɗiyar hanya ce ta bayar da magani a Ƙasar Hausa. Ta wannan siga ana shiga daji a samo sassan bishiyoyi ko ciyayi, a yi amfani da su wajen magance cuta. Wannan hanya ta amfani da itatuwa wajen yin magani hanya ce mai kyau sosai. Yana ma da matuƙar muhimmanci masana kimiyyar harhaɗa magunguna su duƙufa sosai wajen gano irin ɗimbin alfanu da za a iya samu a cikin samar da magani daga ɗimbin bishiyoyi da ciyayin da Allah ya hore wannan yanki na Ƙasar Hausa mai albarka. Tabbas yin hakan zai ƙara haɓɓaka tattalin ariziƙin ɗaiɗaiku, har ma da gwamnatoci sannan kuma ya samar da guraben ayyukan yi.
Wannan hanya ta bayar da magani ta hanyar itatuwa tana da faɗi. Tana da rassan da suka haɗa da:
  • Sassaƙe-Sassaƙe: Hanya ce ta bayar da magani a Ƙasar Hausa da ake sassaƙo jikin bishiya. Sannan a shanya shi ya bushe daga baya kuma a daka ana sha, kodai ta hanyar jiƙa shi da ruwa kai tsaye, ko kuma ta hanyar zubawa a abinci ko abin sha kamar irin su kunu, koko, fura da sauransu.
  • Ciyayi da Ganyayyaki: Akan samu ciyayi ko ganyayyakin bishiyoyi a shanya su, su bushe, sannan a daka su, su zama gari. Bayan an mayar da su gari sai a riƙa zubawa a ruwa, ko abinci, ko abin sha, sannan a riƙa sha.
  • Jiƙo: A nan kuma akan samu wani ɓangare na bishiya wand aka iya zama saiwa, ko ɓawo, ko sassaƙen jikinta, ko wasu ganyayyaki, ko ciyayi a zuba a cikin tukunyar ƙasa, ya jiƙu, sannan a riƙa sha ana wanka don samun waraka daga wata cuta.
  • Turare: Hanyar magani ce da ake samun itatuwa, ko ciyayi, ko ganyayyaki, a wasu lokutan akan daka su, su zama gari, wasu lokutan kuma a ɗan dandaƙa su a riƙa zuba wa a cikin garwashin wuta, sannan a rufe dukkan jiki da mayafi, a riƙa shaƙar hayaƙin, da haka ake samun lafiya.

Sannan kuma akwai turaren da shi a gurin ake ajiye shi, hayaƙin ya dabaibaye ko’ina. Ta wannan hanyar maras lafiya ya ke samun sauƙi.

  • Sirace: Hanya ce ta bayar da magani da ake tafasa magani a tukunya, wanda wannan magani na iya zama ciyayi, ganyayyaki, saiwoyi, ko sassaƙe. Bayan ya tafasa yana tururi, sai a juye a mazubi sannan a lulluɓe mutum da magani ta yadda iska ba za ta riƙa fi taba. Wannan tururin sai ya ratsa jikin mutum. Ana buɗe mutum za a ga ya haɗa gumi larkab.
  • Salala: Hanyar bayar da magani ce da ake samun garin magani wanda ka iya zama na ganye ne, ko ciyawa, ko sassaƙen bishiya, ko saiwa da sauransu. Sai a samu gari wanda ka iya zama na maiwa, jar dawa, da sauransu, a riƙa yin kunu maras kauri, ana baiwa maras lafiya yana sha, da haka har ya warke.
  • Shafe-Shafe: Hanyar bayar da magani ce da ake amfani da mai ko kuma cakuɗa man da wani garin magani. Akan samu wannan mai ko dai daga jikin dabbobi, kamar man shanu, ko bishiya, kamar man kaɗe/man kaɗanya, ko kitsen kaji, zaki, da sauransu. Ana iya shafa man shi kaɗai, ko kuma a cakuɗa shi da wani garin magani, sannan a riƙa shafawa a gurin da cutar take.

Magani ta Hanyar Amfani da Ƙasa

Idan aka ce ƙasa a nan, ana nufin abin da ya shafi ƙasa kai tsaye. Kanwa, jar kanwa, dukkannin su ƙasa ce. Ana amfani da su wajen yin magani. Ko dai ta hanyar shan su kai tsaye, ko kuma ta hanyar haɗa su da wasun su.

Magani ta Hanyar Bori da Tsafi

Bori da tsafi  bagargajiyar hanya ce ta neman waraka daga cututtuka da suka shafi aljanu a Ƙasar Hausa, wacce daga baya, bayan zuwan Musulunci Ƙasar Hausa da kuma tasirinsa, ya saka wannan hanya ta zama abar ƙyama. Ta wannan hanya mutane ke yin amfani da salon bori, da tsafi da sauransu.

Magani ta Hanyar Tsibbu

Kalmar tsibbu daga kalmar (طِبُّ) ce. Wacce ta ke Balarabiyar kalma ce aka jirkita ta, ta koma tsibbu, wanda a Larabcen ta ke nufin magani. To haka nan a Hausancen ma.
Hanya ce da malamai ke amfani da addu’o’i, da rubutu (a rubuta wasu surori, ko ayoyin alƙur’ani, ko wani hatimi, a jikin allo, ko wata takarda) wajen bayar da magani.
Masu bayar da magani ta wannan hanya su ke bayar da rubutun sha, hatimi a rufa laya, ko guru, ko daga, ko rataye, ko karantawa da sauran makamantansu.

Magani da Wuta

Wannan hanyar bayar da magani ta karkasu kamar haka:
  • Sakiya: Sakiya hanya ce da ake magance cututtukan da suka shafi fata kamar ƙurji da sauransu. A nan akan samu allura ko wani ƙarfe a saka shi a cikin wuta ya yi ja, sannan a ɗauko a tsikara a kan ƙurji, sai ya fashe, ruwan da ke cikinsa ya zube.
  • Allura: Ita kuma hanya ce da ake saka allura a cikin wuta, idan ta yi ja sai a ɗauko a ɗora a ƙirjin mutum.

Magani ta Hanyar Tsagu

Hanya ce da ake magance cuta ta hanyar tsattsaga jikin mutum. Akwai wacce ake kira ɓalli-ɓalli, wacce ake samun aska a yi wa mutum tsage-tsage a ƙirji daga ƙasan nono, akwai kuma wacce ake bin dukan gaɓoɓin jikin mutum a yi tsaga kamar guda biyu-biyu da aska.

Magani da Ƙaho

Hanya ce da ake samun ƙahon Saniya ko wata dabbar a fiƙe, sannan a yi masa ƙofa, sai a riƙa kafa shi a jikin mutum. Idan jini ya taru sai a cire ƙahon, a tsattsaga, sannan a sake mayar da ƙahon, a zuƙo jinin.

Masu Bayar da Magani

Akwai rukunin mutane da dama da suke bayar da magani a Ƙasar Hausa. Daga cikinsu akwai waɗanda su ka shafi sana’o’i, akwai kuma waɗanda su sana’ar bayar da maganince ta su sana’ar. Daga cikin irin waɗannan mutane akwai:
  1. Magori: Mutum ne da ke shiga da ji ya samo magani wanda ka iya zama kowane nau’i na magani, sannan ya sarrafa shi ta hanyar da ta ce, kamawa da mayar da shi gari, da sauransu.

    Bayan sun samo maganin kuma sukan bi hanyoyi biyu: ko dai su riƙa bi kwararo-kwararo, layi-layi suna tallen maganin, ko kuma su ka sa maganin a kasuwa suna sayarwa. Bayar da magani ita ce sana’ar magori.

  2. ‘Yar Mai Ganye: A taƙaice ana iya cewa ‘yar mai ganye macen magori ce. Mata ne da kan zuba magani a ƙwarya suna bi gida-gida suna bayar da magungunan da suka shafi mata da kuma ‘yan sauran cututtukan da ba za a rasa ba. Bayar da magani ita ce sana’ar ‘yar mai ganye.
  3. Wanzamai: Wanzamai su ne manyan masu bayar da magani a Ƙasar Hausa. Sukan bayar da maganin cututtuka da dama. Sana'ar wanzanci ita ce sana’ar wanzamai.
  4. Maƙera: Maƙera ma suna bayar da maganin da ya shafi wuta. Su ke yin sakiya, sannan kuma su na bayar da maganin ƙunan wuta. Wato inda mutum ya ƙone, maƙera ke bas hi maganin wuta. Sanar ƙira ita ce sana’ar maƙera.
  5. Mahauta: Mahauta su ke bayar da maganin yanka da kuma maganin sukar ƙaho. Wato idan mutum ya yanke, ko wata dabba mai ƙaho kamar Saniya ko rago ta soke shi da ƙahonta, sai a je gurin mahauta a karɓo masa magani. Fawa ita ce sana’ar mahauta.
  6. Mafarauta: Kasancewar Mafarauta mutane ne masu hulɗa da daji, su ke bayar da maganin da ya shafi cizon maciji, ko kunama, ƙarfe, ƙaho da sauransu. Farauta ita ce sana’ar mafarauta.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M (1992). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Qananan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Ziyarar Gani da Ido Zuwa Kasuwar Garki da ke Cikin Jahar Jigawa a Najeriya. A rana Juma'a, 16/12/2016.

Darrusan Hausa

  • Darrusan Hausa

  • Ƙasar Hausa



    Musulunci


    Zuwan Turawa


    Tarbiyya


    Bukukuwa


    Wasanni


    Kayan Kiɗan Hausa



    Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


    Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



    Sauran Shafukanmu:

    Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub