Nahawun Hausa: Nunau

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Nunau


Gabatarwa

Kalma ce da ake amfani da ita wajen yin nuni. Nunin kuma kan iya zama mutum, guri, kaya, ko wani abu da ya yi kama da wannan wanda kuma zai iya kasancewa a kusa ko a nesa. Kalmomin nuni sun haɗa da wannan, wancan, waɗannan, waɗancan, nan, da kuma can.

Ma’anar Nunau

Yahaya, Zariya, Gusau da ‘Yar’aduwa (2007), suka ce: “Kalma ce da ke nuna abu dangane da nisarsa ko kusancinsa da mai magana”.

Rabe-Raben Nunau

Kashi biyu ne kuma ta fuska biyu:

  1. Kusanci da kuma nisa: Su ne kalmomin nunau da ake amfani da su wajen nuna kusancin wanda ake magana da shi ko kuma nisa. Misali:
    • Wannan gidan yana da kyau.
    • Waɗannan gidajen suna da kyau.
    • Zauna a nan.
    • Ga shi can a gefen rumfa.
    • Wancan yaron yana da ƙwazo.
    • Waɗancan yaran suna da hazaƙa.
    • Waccar yarinyar tana da haƙuri.

    Tsokaci: Idan muka lura da kalmomin wannan, waɗannan, da kuma nan, duk sun yi nuni ne da kusancin mai magana a cikin jimlolin da suka bayyana. Wancan, waɗancan, da kuma can, su kuma sun yi nuni ne da nisan da suka yi da maimagana.

  2. Jama’i da kuma tilo: Daga cikin kalmomin nuni akwai masu nuni zuwa ga abubuwa masu yawa; waɗannan kalmomi su ne waɗannan da kuma waɗancan, to, sun zama jama’i kenan. Sai kuma wannan da kuma wancan waɗanda suke nuni da abu guda. Waɗannan kuma su ne tilo.

Tsinkaye: Babu bambancin tsakanin jinsi mace da na namiji wajen amfani da kalmomin nuni in banda muhalin da ake nuna mace ɗaya da take nesa da mai magana kamar yadda ya zo a cikin jimlar ƙarshe ta jimlolin da aka kawo a misalan da suke a sama.

Sannan kuma dai waɗannan kalmomi na nunau sukan zo a matsayinwakilin sunaa cikin jimla kamar yadda ya zo a Junaidu da ‘Yar’aduwa (2002) da kuma Sani (2009). Misali:

  1. Wannan yaro.
  2. Wannan yariya.
  3. Waɗannan yara.

Manazarta:


Junaidu I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002). Harshe da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan - Nigeria.

Sani M. A. Z. (2009). Siffofin Daidaitaciyyar Hausa. Becnhmark Publishers Limite, Kano – Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub