Rumbun Ilimi - Nazarin Rubutacciyar Waƙa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Nazarin Rubutacciyar Waƙa


Gabatarwa

Ita dai waƙa wata aunanniyar magana ce, kamar yadda ya zo a Junaidu da ‘Yar’aduwa (2002). Ita kuwa rubutacciyar waƙa, rubutata ake yi koma da za a rera ta daga baya (Ɗangambo, 1984). Waƙa, aba ce mai ma’aunin da sai ta hau kansa kafin ta zama cikakkiyar waƙa. A wannan darasi, za mu duba yadda manazarta za su nazarci rubutacciyar waƙa domin samun cikakkiyar fahimta game da ita.

Ana nazartar rubutacciyar waƙa ta hanyar lura da waɗannan ma’aunai kamar haka:

  1. Jigo.
  2. Zubi da Tsarin Waƙa.
  3. Salon Sarrafa Harshe.

Jigo

Jigo shi ne asalin gundarin saƙon da marubucin waƙa yake son isarwa ga makarantansa ko masu sauraronsa, wanda ake gina waƙar kacokaf a kansa, wanda kuma yana iya kasancewa wa’aztarwa, faɗakarwa, wayar da kai, gargaɗi, soyayya, da sauran abubuwan da suka shafi rayuwar ɗan’adam ta duniya da lahira.

Zarruƙ, Kafin Hausa da Alhassan (2010), sun bayyana cewa daga cikin rubutattun waƙoƙi akwai waɗanda jigoginsu na addini ne da kuma waɗanda a kan al’amuran duniya aka gina su. Waƙoƙin madahu – waƙoƙin yabon Annabi (S.A.W.), waƙoƙin gargaɗi, waƙoƙin da ke karantar da yadda za a yi addini da sauransu duk waƙoƙi ne da jigonsu ya zama addini. Sauran waƙoƙi irin na siyasa, soyayya, wayar da kai, da sauransu, su kuma a kan al’amuran duniya aka gina jigonsu.

Saboda haka a nan; wato abin da ya shafi nazarin jigon rubutacciyar waƙa, manazarci zai yi iya bakin ƙoƙarinsa ya gano:

  1. Jigon Waƙa: Wannan na nufin mai nazarin waƙa ya zurfafa tunani ya zaƙulo ko fito da asalin baiti ko baitocin da ke ɗauke da saƙon da waƙar ke isarwa a fili.
  2. Warwarar Jigo: Warwara a nan tana nufin yin bayani dalla-dalla tare da ƙarin haske game da saƙon da waƙa ke isarwa ta hanyar kafa hujjoji daga baitukan waƙar.  
  3. Bayanin Jigo: Wannan na nufin yin bayani dalla-dalla kuma daki-daki a jerance kan hanyoyin da mawaƙi ya bi wajen isar da saƙonsa a cikin waƙar.

Zubi da Tsarin Waƙa

Zubi da kuma tsarin waƙa, shi ne abin da wasu marubutan suka kira Salo, wanda kuma yake magana game da yadda aka ƙera ko gina waƙa. Abin nufi a nan shi ne irin salo, yanayi da kuma tsarin da aka zuba ko aka tsara waƙar a kai. Wannan kuma ya shafi abubuwan da suka haɗa da ɗango, baiti da kuma ƙafiya ko amsa-amo.
Ɗango: Shi ne ɗaiɗaikun layuka ko saɗara da ke cikin waƙa waɗanda suke haɗuwa su samar da baiti. Wato a cikin baiti ɗaya za a iya samun ɗangwaye biyu, uku, huɗu ko biyar.
Baiti: Shi ne haɗaka ko jimillar ɗangwaye a waje guda. Baiti yana samuwa daga ɗangwaye biyu zuwa biyar.
Ƙafiya ko Amsa-Amo: Ita ce muryar da baiti ko ɗangon waƙa yake ƙarewa da ita wadda ka iya zama harafi ko kalma.

A wannan gaɓa, mai nazarin rubutacciyar waƙar Hausa zai nazarci waɗancan abubuwa guda uku da aka zayyana a sama kamar haka:

Ɗango

Shi ɗango a fannin nazarin rubutacciyar waƙar Hausa ana duba yawansa da kuma tsarin zubinsa. A ƙai’adar rubuta waƙar Hausa, ana zuba ɗangwaye biyu-biyu ne, uku-uku, huɗu-huɗu ko kuma biyar-biyar a cikin baiti guda. Wannan yawan ɗangwaye har-ila-yau da su ake amfani wajen yi wa waƙa rukuni, akwai rukunin waƙa da ake kira Ƙwar-biyu ko ‘Yartagwai, wadda ita ce waƙa mai ɗangwaye biyu a cikin baiti ɗaya. Waƙa mai ɗangwaye uku a cikin baiti ɗaya sunanta Ƙwar-uku. Mai huɗu-huɗu kuma sunanta Ƙwar-huɗu. Sai kuma mia biyar-biyar wadda ake kira Ƙwar-biya.

Tsarin Baitoci

A nan, ana son manazarci ya nazarci irin salo da aka yi amfani da shi wajen zuba baitukan waƙa. A fagen rubutun waƙar Hausa, akwai wasu tsarurruka ko salo da ake bi wajen zuba baitukan waƙa tun daga farkonta har zuwa ƙarshenta ba tare da saɓawa ba. Wannan, yana daga cikin abin lura wajen zamowar waƙa mai inganci. Rashin bin wannan ƙa’ida yana kai wa ga rage darajar waƙa. Ga yadda abin yake:

Baiti Mai Ɗangwaye Biyu: Ana rubuta baitocin wannan waƙa kamar haka:

Na fara talifi da sunan Ubangiji,
           Subhanahu Mannanu babu kamar Shi.
Komi ka gan shi a duniya farko garai,
           Ko ka gaya mini Rabbu waffare Shi?
Duk wanda yai farko akwai ƙarshe garai,
           Sai rai guda ne babu mai kaushe Shi.
An ciro wannan daga littafi mai suna Waƙoƙin Mu’azu Haɗejia, shafi na 27, wallafar Northern Nigerian Publishing Company, Zaria.

Baiti Mai Ɗangwaye Uku: Mawaƙa suna rubuta ɗangwayen wannan baiti a jere ɗaya-a-ƙasan ɗaya. Ga wani misali da aka ciro daga littafin Junaidu da ‘Yar’aduwa (2002), mai suna Harshe da Adabin Hausa a Kammale don Manyan Makarantun Sakandire shafi na 133:

Dukkan masaɓi bai ƙure saɓon Ka ba,
Ya fita ya ƙara Kai ba zai wuce Ka ba,
           Sai shi ya hallaka Kai kuma Kana matsayinKa.

Da yawa misalai wanda ba su ƙidayiwa,
Mulkin cika Fir’auna sai da sha ruwa,
           Sannan ya sha ya halaka saboda isar Ka.

Da duniya duka za mu taru mu tabbata,
Duka ayyukan saƙo mu bas-su mu gaskata,
           Wallabi ni na yarda ba ni da suka.

Baiti Mai Ɗangwaye Huɗu-Huɗu: Ana rubuta wannan waƙa ta sigogi guda biyu. Na farko, ana rubuta baituka masu ɗangwaye huɗu-huɗu ta hanyar jeranta ɗangwayen daga sama zuwa ƙasa a jere. Ga wani misalai da muka ciro daga littafin Junaidu da ‘Yar’aduwa (2002), mai suna Harshe da Adabin Hausa a Kammale don Manyan Makarantun Sakandire shafi na 134:

Rabbana Kai min ijaba,
In yi waƙa mai sawaba,
Sha biyar ga watan Satumba,
Mun yi murna har da zarya.

Shekara hamsin cikar ta,
Sai dai tara ga dubunta,
Shekaru shida ɗoriyarta,
Kamar mu manta riƙe ƙidaya.

Sai kuma wata hanyar da ake rubuta ɗangwayen a bisa tsarin hannun riga biyu dama biyu kuma hagu tare da kiyaye cewa, ɗangon farko shi ne layi na farko daga hagu, na biyu kuma a sama daga dama. Ga wani misali da aka ciro daga  waƙar Mu’azu Haɗejia a littafi mai suna Waƙoƙin Mu’azu Haɗejia, shafi na 27, wallafar Northern Nigerian Publishing Company, Zaria.

Karuwa kafirar dangi,                  Ki saurara ki sha zagi,
Takocilo mai kamar tsagagi,        Na Ingila ba na nan kusa ba.

Uwarta, ubanta sun ƙi ta,           A dangi babu mai son ta,
Baƙar aniya ta cuce ta               Haƙiƙa ba da ƙarya ba.

Ta ce ita ce ɗiyar iska,              Tana nan gobe sai Maska,
Tana yawo a karauka,               Wajen baɗi sai ta je Kalba.

Baiti Mai Ɗangwaye Biyar-Biyar: Ana rubuta baitukan wannan waƙa ta siga biyu, kodai ta hanyar zuba dukan ɗangwayen a jere daga sama zuwa ƙasa, ko kuma ta hanyar yi musu tsarin dama da hagu sannan na ƙarshe a rubuta shi a tsakiya daga ƙarshen ƙasa kamar haka: Ga wannan misalai daga littafin Junaidu da ‘Yar’aduwa (2002), mai suna Harshe da Adabin Hausa a Kammale don Manyan Makarantun Sakandire shafi na 137:

Randa anka rabe takardu,
Duk halitta za ta sadu,
Gun hukunci har da shaidu,
Ga Raƙibu zuwa Atidu,
Da ba sui saɓon Ubangiji ba.

Ayyukan irin na kirki,
Inda kai ko da a ɗaki,
Sun rubuta ko tafarko,
Ko da hannu ko da aiki,
Aikin hairi ba sui rufi ba.

Sai kuma ɗaya sigar wadda muka ciro wani misali daga waƙar Sa’adu Zungur a littafi mai suna Waƙoƙin Sa’adu Zungur, shafi na 6, wallafar Northern Nigerian Publishing Company, Zaria.

Mu yi salatu da sallamawa,                Ga fiyayyen Annabawa,
Wanda ya shige kwaikwayawa,           Shugaban duka jarumawa,

A gare shi muke biɗar fakewa.

Allah ɗai ad-da ƙudura,                       Mulki, iko, da nasara,
Babu tasiri da sutura,                          Ba tsimi, kuma ba dabara,

Ga sadaukai, Soja, askarawa.

Ƙafiya Ko Amsa-Amo

Ita ce muryar da baiti ko ɗangon waƙa yake ƙarewa da ita wadda ka iya zama harafi ko kalma. Tana da dawamammen tsarin da ake zuba waƙa a kansa. Ƙafiya, tana iya zamowa a ƙarshen kowane ɗango na baiti ko kuma ƙarshen kowane baiti na waƙa. Idan aka fara waƙa da ƙafiyar ɗango, to dole ne ta ƙare da haka, haka nan ma idan aka fara waƙa da ƙafiya a ƙarshen baiti da haka za ta ƙare. Sai dai, akwai sigogi uku da Junaidu da ‘Yar’aduwa (2002), suka zayyano, waɗanda ake yin ƙafiya a bisa tsarinsu kamar haka:

  1. Ƙafiya ko Amsa-Amon Ƙarshen Baiti: Ita ce ƙafiyar da ke zuwa a ƙarshen baitin waƙa. Daidai ne da baiti mai ƙwar biyu, uku har zuwa biyar. Ga wani misali daga waƙar Mu’azu Haɗejia:

    Na fara talifi da sunan Ubangiji,
                  Subhanahu Mannanu babu kamar (Shi).
    Komi ka gan shi a duniya farko garai,
                  Ko ka gaya mini Rabbu waffare (Shi?)
    Duk wanda yai farko akwai ƙarshe garai,
                  Sai rai guda ne babu mai kaushe (Shi).

    Idan muka lura da ƙarshen waɗannan baituka ‘yan ƙwar-biyu da ke sama, za mu lura da cewa, kowane baiti ya ƙare da harafin Shi. Wannan ita ce ƙafiyar harafi.

    Ga kuma wani misalin da aka ciro daga littafin Junaidu da ‘Yar’aduwa (2002), mai suna Harshe da Adabin Hausa a Kammale don Manyan Makarantun Sakandire shafi na 139:

    Muna gode Allahu Sarkin sarauta,
    Da Yas sa mu jimlar mutanen (sawaba).

    Fa mun roƙi Allahu Sarki Ta’ala,
    Ya taimaki mai taimakon ‘yan (sawaba).

    Na sani wadata da hutu da ‘yanci,
    Cikakken mutunci sabilin (sawaba).

    Idan muka lura da ƙarshen waɗannan baituka da ke sama, za mu ga cewa sun ƙare ne da kalmar sawaba. Wannan ita ce ƙafiyar ƙarshen baiti amma mai ƙarewa da kalma. Haka abin yake a dukkan muhallin da ya dace a ajiye ƙafiya.

  2. Ƙafiya ko Amsa-Amon Ciki da Waje: Ita ce ƙafiyar da take zuwa a ƙarshen kowane ɗango da kuma baiti. Wato ɗango yana ƙarewa da ƙafiya, haka nan ma baitin. Duba wannan waƙa ta Mu’azu  Haɗejia da aka ciro daga littafi mai suna Waƙoƙin Mu’azu Haɗejia, shafi na 27, wallafar Northern Nigerian Publishing Company, Zaria.

    Karuwa kafirar dangi,                   Ki saurara ki sha zagi,
    Takocilo mai kamar tsagagi,         Na Ingila ba na nan kusa ba.

    Uwarta, ubanta sun ƙi ta,              A dangi babu mai son ta,
    Baƙar aniya ta cuce ta,                 Haƙiƙa ba da ƙarya ba.

    Ta ce ita ce ɗiyar iska,                 Tana nan gobe sai Maska,
    Tana yawo a karauka,                 Wajen baɗi sai ta je Kalba.

    Idan muka lura da ƙarshen kowane ɗango na kowane baiti, za mu gan shi ɗauke da ƙafiya, duk da cewa ba wai harafi guda ne ya bibiyi dukkan ɗangwayen cikin baitukan waƙar ba tun daga na farko har zuwa ƙarshe, amma dai dukkan baiti ɗangwayen cikinsa suna ɗauke da ƙafiya iri guda. Misali, ɗangwayen cikin baitin farkon suna ɗauke da sautin harafin gi, na biyu kuma ta, na uku kuma ka. Su kuwa dukkan baitukan waƙar tun daga na farko har zuwa na ƙarshe, da sautin harafin ba suke ƙarewa. Latsa nan ka zanarci waƙar.

  3. Hawainiyar Ƙafiya ko Amsa-Amo: Wannan ƙafiya ita ce wadda take zuwa da sauti ko amo guda a ƙarshen kowane ɗango na baiti da kuma shi baitin a kan-kansa. Wato ƙafiyar ɗango da baiti duk iri ɗaya ce. Sai dai, tana bambanta daga baitin farko zuwa na gaba. Wato kenan kowane baiti yakan zo da ƙafiyarsa ta daban. Ga wannan misali da aka ciro daga littafin Junaidu da ‘Yar’aduwa (2002), mai suna Harshe da Adabin Hausa a Kammale don Manyan Makarantun Sakandire shafi na 142:
  4. Turawa sun ga Afirkanmu,
    A mafarki har suka neme mu,
    A yaƙini yau suka same mu,
    Domin himma da yawan ilmu,
                  Suka sadu da sababbin ƙaumu.

    Sun ƙetare kogi da sahara,
    Mil dubbai sunka ci asfara,
    Da Afirkan mai masu jagora,
    Suka wo nazarin duka akdara,
                  Na Afirka cikin wannan marra.

    Haka sunka shigo mana Afirka,
    Suka sami ƙasa mai albarka,
    Mai yalwa mai daɗin iska,
    Da wajen noma garka-garka,
                  Da mutane kowa na harka.

    Idan muka lura da kowane ɗaya daga cikin waɗannan baituka guda uku, za mu fahimci dukkan ɗangwayen cikin baitin guda biyar sun ƙare ne da amsa-amo ko ƙafiya iri guda. Na farko ya ƙare da mu, na biyu kuma ra, sai na uku ka. Irin wannan nau’in ƙafiya ita ake kira hawainiyar ƙafiya. An kuma kira ta da wannan suna saboda sassauyawa da take yi idan baiti ya sauya kamar yadda hawainiya take rikiɗa idan ta canja guri.

Salon Sarrafa Harshe

Salon sarrafa harshe a nan na nufin irin sigar da marubucin waƙa ya yi amfani da ita wajen amfani da kalmomi a cikin waƙarsa. Ana so marubucin waƙa ya yi amfani da sassauƙar Hausa tare kuma da zaɓe da jera kalmomin da suka dace a kuma muhallin da ya dace. Misali, idan waƙar ta shafi yabo, to zai dace a yi amfani da kalmomin da za su fito da daraja da martabar wanda ake yi wa waƙar. Duba waƙar Yabon Ubangiji ta Mu’azu Haɗejia. Haka nan ma gargaɗi, wayar da kai, jan hankali da sauransu, kowace tana da kalmomi keɓantattu da suka dace a yi amfani da su wajen rubuta waƙar.

Ƙari a kan haka kuma, ana lura da yin amfani da adon harshe, wanda yake da ma’ana ta yin amfani da kalmomin da suka shafi karin magana; kwatanta mutum da wata halitta a fagen jarumtaka, kyau ko haƙuri; zambo; habaici da sauransu kuma a muhallan da suka dace. Waɗannan suna matuƙar ƙarawa waƙa kwarjini da nishaɗi.

Haka nan ma dai, ana lura da yawan gauraya kalmomin Hausa da na Larabci ko kuma shi kansa Karin Hausar wani gari kamar a ce Sakkwatanci, Katsinanci da sauransu.

Waɗannan abubuwa da aka zayyano a dunƙule guda uku; jigo, salo da zubi da kuma salon sarrafa harshe, su ne muhimman abubuwan da manazarcin rubutacciyar waƙa yake binciken ƙwaƙwaf a kan su game da waƙa. Wannan kuma domin feɗe biri har wutsiya game da wannan waƙa domin a yi mata kyakkyawar fahimta.

Manazarta:


Junaidu I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002). Harshe da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan - Nigeria.

Mu’azu Haɗejia M. (1980). Waƙoƙin Mu’azu Haɗejia. Northern Nigerian Publishing Company, Zaria, Kaduna-Nigeria.

Yahaya I. Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M. (2007). Darrusan Hausa Don Manyan makarantun Sakandare 1. University Press PLC, Ibadan, Nigeria.

Yahaya I. Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M. (2007). Darrusan Hausa Don Manyan makarantun Sakandare 2. University Press PLC, Ibadan, Nigeria.

Yahaya I. Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M. (2007). Darrusan Hausa Don Manyan makarantun Sakandare 3. University Press PLC, Ibadan, Nigeria.

Zungur A. M. S. (1981). Waƙoƙin Sa’adu Zungur. Northern Nigerian Publishing Company, Zaria, Kaduna-Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare, Littafi Na Biyu. University Press, Ibadan, Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare, Littafi Na Uku. University Press, Ibadan, Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub