Sadarwa: Gaurayen Gaɓɓai

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sadarwa: Gaurayen Gaɓɓai


Gabatarwa

Bahaushe kan gauraya gaɓɓansa a wasu lokutan idan aka samu yanayin da gaɓa guda bata isa ba wajen sadarwa.  Misali, idan Bahaushe yana son ya ce da kurma “tafi ka dawo gobe”. Sai ya miƙar da hannunsa, sannan ya kaɗa shi gaba, sai kuma ya karkatar da kansa zuwa kafaɗarsa, sai kuma ya tallabi kan da tafin hannunsa tare da linshe idanuwansa. Wannan shi ne ke nuna waccar maganar da muka faɗa a sama. Ga kaɗa daga cikin irin waɗannan alamomi na sadarwa.

  1. Ɗora fuska a tafin hannu tare da linshe idanuwa na nufin barci.
  2. Riƙe ɗefin kunne ta ƙasa sannan a jijjiga kunnen, wannan na nufin gargaɗi.
  3. Ɗora yatsa a kunne sannan a kewaya bayan kunnen da shi, wannan na nufin ƙaryata magana.
  4. Karkaɗa yatsu biyu; manuni na dama dana hagu suna yin sama da ƙasa a saɓe, wannan na nuna gudu.
  5. Taɓa tsinin harshe da yatsa ɗaya na nufin ɗanɗano.
  6. Taɓa tsinin harshe da yatsa ɗaya sannan a furzar, wannan na nufin ɗaci.
  7. Zozar kunci da yatsa ɗaya na nufin daɗi ko zaƙi.
  8. Tsuke yatsun hannun dama sannan a riƙa kai su baki. Wannan na nufin cin abinci.
  9. Ɗora fuska a tafin hannu, sannan a ɗaga a kuma nuna baya da babban yatsa sau ɗaya, wannan na nufin jiya. Sau biyu kuma shekaran jiya.
  10. Miƙar da tafin hannun hagu sannan a riƙa cusa shi tsakanin manuni da babban yatsan hannun dama wannan na nufin ƙirgar kuɗi.
  11.  Rufe baki, sannan a ɗora manuni a tsakiyar bakin wannan na nufin a yi shiru.
  12. Juya fuska tare da harba hannu sama na nufin babu ruwana ko ban sani ba.
  13. Ɗora tafin hannu a ƙofar hanci ana shinshinawa na nufin ƙanshi.
  14. Sosa wani sashe na jiki na nufin ƙaiƙayi.
  15. Ɗora hannaye biyu a ka na nuna shiga cikin halin damuwa.

Manazarta:


Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake Da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo Da Koyarwa. Ibrash Islamic Publications Centre L.T.D., 31 Adalabu Street, Surulere, Lagos.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2011). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Ɗaya. University Press PLC, Ibadan, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub