Sadarwa: Amfani da Kafaɗa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sadarwa: Amfani da Kafaɗa


Gabatarwa

Ana amfani da kafaɗa wajen ƙin amincewa da abu da kuma nuna isa:

  1. Ƙin Amincewa: Ana nuna ƙin amincewa da abu ta hanyar jijjiga kafaɗa ɗaya. Ana kuma jijjiga kafaɗa ne ta hanyar ɗaga ta sama sannan a sauke ƙasa da sauri.
  2. Jin Kai: Idan Bahaushe ya ɗaga kafaɗarsa sama a lokacin da yake tafiya, to yana nuna cewa ya kai ko kuma shi ya tumbatsa koda kuwa a fannin kwalliya ne.

Manazarta:


Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake Da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo Da Koyarwa. Ibrash Islamic Publications Centre L.T.D., 31 Adalabu Street, Surulere, Lagos.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2011). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Ɗaya. University Press PLC, Ibadan, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub