Sarrafa Harshe

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarrafa Harshe


Gabatarwa

Sarrafa harshe ɗaya ne daga cikin rassan adabin baka. Masana harshen Hausa sun bambanta wajen ambaton wannan reshe na Adabin Baka. Farfesa Ɗangambo (1984), ya ambace shi da Hikima da Sarrafa Harshe, wanda daga nan muka ciro wannan sunan. Sai kuma Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yar’aduwa (1992), da suka kira shi da suna "Azancin Magana". Haka nan ma su Zarruƙ, Kafin Hausa, da Alhassan (1987), sun ambace shi da "Salon Magana". Amma dukkansu sun yarda da, da zamowar:

Abubuwan da ke ƙunshe cikin wannan reshe na adabin baka.

Sarrafa harshe salo ne da Bahaushe yake amfani da shi wajen sarrafa magana ta sigogi mabambanta da ke ƙayatar da zance ko kuma isar da wani babban saƙo amma ta cikin hikima kuma a wasu 'yan kalmomi dunƙulallu. Da su ake yiwa zance (na baka ko a rubuce) ado; adon harshe.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Ɗaya. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub