Tarihi

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tarihi


Gabatarwa

Tarihi, kalma ce da aka aro ta daga Larabci (تاريخ), wacce ke da ma’ana ta labarin da ya faru a wani lokaci da ya wuce. Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yar’aduwa (1991), suka ce, “Tarihi labari ne na haƙiƙa dangane da wasu abubuwan da suka taɓa faruwa na al’umma”.

Saboda haka kenan, ana iya cewa shi tarihi labari ne na gaskiya ba ƙirƙirarre ba kamar almara, tastuniya ko hikaya, waɗanda su ƙiƙirarsu ake yi.

Misali, a cikin wannan Rumbu  na Ilimi akwai tarihin masarautu kamar irin su Kano, Dutse, da sauransu. Haka nan akwai tarihin ɗaiɗaikun mutane kamar irin su Sir Ahmadu Bello da sauransu.

Muhimmancin Tarihi

Babban amfanin tarihi shi ne nazartar rayuwar da ta gabata don samun abin koyi daga abubuwan da suka zo na kyau a ciki, nisantar abubuwan da ba su da kyau, ɗaukar darasin rayuwa dan kaucewa abin ƙi, da sauran makamantansu.

Tarihi yana da matuƙar muhimmanci ta kowace fuska, saboda a cikin tarihi ake sanin asali ko tushen kowane abu. Daga ciki kuma har da nasara da akasin haka. Dukkan addinai sun baiwa tarihi kulawa ta musamman. Allah yakan ambatawa Annabawa da sauran jama’a labaran al’ummun da suka gabace su dan yin koyi da kyawawan ayyukansu da kuma nisantar munanan ayyukansu, saboda gujewa faɗawa irin halin da suka faɗa, ko kuma kwaɗaitar da su samun abin da suka samu.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’, Gidan Sa’adu Zungur, Kano – Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub