Rumbun Ilimi - Waƙa Gargaɗi

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Waƙa Gargaɗi: Na'ibi Sulaimanu Wali


Subhannallahi me za na ce,
              Zamanin nan namu ya rikice.

Mahankalta sun haukace,
              Ma biya sunna sun ɗau fice.

Mai basira duk ta daƙushe,
              Mai bin hanya ya karkace.

Likitan cuta mai magana,
              Cuta ta kada da shi zai mace.

Ba amana, ba son gaskiya,
              Kowa sai ƙulle-ƙulle.

Jahilci ya yi yawa ga-ma,
              Ilimin Allah ya mace.

Har an binne shi wajen gari,
              Mai zuwa niyya tasa ɓace.

Babu mai aiki bisa zuciya,
              Ɗaya don Allah sai don a ce.

Imani ya ƙare gama,
               So domin Allah ya mace.

Sai don samu don arziƙi,
              Yadda za a yi zance-zance.

Ba a son zancen gaskiya,
              In kana yi kai ne mai fuce.

Kai ne sususu sakarai,
              Wayonka kaɗan ka haukace.

In ka ce Allah, ko Annabi,
              Su ne suka ce kuma sai a ce.

Kai ne ka fi kowa ko kuwa,
              Wa ce ka ga ɗan Sarkin fice.

Kowa burinsa ya san kuɗi,
              Ga gida ga mota ga mace.

Ko ya hau rali sai ya kaikace,
              Yai wajen Sabon Gari ya ɓace.

A cikin wanka a cikin diras,
              Da kayan ƙwambo an ƙwambace.

Yana ta nishaɗi ga giya,
              Ya san ni’ima ya haukace.

A wajen hotal da wajen giya,
               Nan zai ƙare a gaban mace.

Sai rawa sai ihu fasiƙai,
              Gabansa gaɗi ba dakace.

In sun sha sun bugu sai su yi,
              Sururun zancensu a haukace.

Kyautarsu maroƙa karuwai,
              ‘Yan iska ‘ya’yan tarkace.

Zakka, Sallah, duka basu yi,
              Sai dai kyautar a faɗi a ce.

Kai mutum yau ka rasa hankali,
              Ka susuce ka haukace.

Jahilci yai maka runduna,
               Ya hana ka ka san ka karkace.

Ka ƙi shawarto ka fanɗare,
              Iblis ya sa ka karkace.

Matan kuwa su ne karuwai,
              Maƙiya Allah mazawa fuce.

Kan dai mace ta zama karuwa,
              Ta lalace tir! Ba mace.

Ayya haka za mu yi ‘yan’uwa,
              Aikinmu dukansa a barkace.

Anya haka shi ne za ya kai,
              Mu limana ba wata karkace.

Ya Ilahi mu Nijeriya,
              Me za mu yi ko me za mu ce.

Mu yi wa kanmu faɗa, mu bi gaskiya,
              Mu bi kan hanya ba karkace.

Mu tsaya tsayuwar mai yin daka,
               Lokacinmu kaɗan ne zai wuce.

Mu sani duk kowa za ya je,
              Zai hisab ranar gaskiya.

Na gode Allah nai yabo,
              A gare shi a nan zan dakata.

Tsira da amincin Rabbana,
               Ga Rasulu da ya hana yin fuce.

Ko za a cane maka wa ya yi?
              Waƙan nan malam sai ka ce.

Na’ibi Wali sunansa ne,
              Kuma Kurawa unguwarsu ce.

Tamat, yau waƙata ta cika,
              Allah sa mu mu bar son yin fuce.



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub