Rumbun Ilimi - Waƙar Ilimi

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Waƙar Ilimi: Mu'azu Haɗejia


Zamanin nan ba mai ƙasaita,
              Sai mai sana’a da biɗar ilmu.

Muna magana da mutan kirki,
               Waɗanda su ke neman ilmu.

Mata da maza, ɗa ko bawa,
               Duka babu hani ga biɗar ilmu.

In gemu bai hana wasa ba,
              Haka ba shi hani ga biɗar ilmu.

Jahilci shi ne abin kunya,
              Ba mai gemu ba wurin ilmu.

Iɗlibul ilma walau bi Sini,
              Hadisi ne na biɗar ilmu.

Ilmud duniya, ilumd dini,
              Su ne ilmani na nemanmu.

Su ne ilmani azimani, duka,
              Wanda ka nema ka samu.

Duka wanda ka nema daidai ne,
              Ba mai zarginka ga son ilmu.

Abin kunya ga Musulmi wanda,
              Ya bar addini don samu.

Duka ya ƙi farilla har sunna,
              Ko oho in ji karankarmu.

Ba ya fatawarsa ta addini,
              Sai zare ido a wurin damu.

Nan za ka ga halin goganka,
              Shi ne farko a wurin kamu.

Shi za a bari ya suɗe ƙwarya,
               Ba ya kunya dodon damu.

Rashin tarbiyya mai kyawu,
              Shi ne cikas a ƙarshenmu.

Innamal ilmu munzus sigari,
              Tun ana yara ka biɗar ilmu.

Shi ne ya fi kyau mai ƙarko,
              Kuma ba laifi gun gemu.

Tauhidi shi ne farko don,
              A sanarsu sun san Mahaliccinmu.

Wajibai, korarru, siffofi,
               Duk wanda ya san haka ya samu.

Hakanan na Ma’ika duk su gani,
               Wajibi ne gun addininmu.

San nan salla babba inji,
              Babban alheri ce gunmu.

Alla ya faɗa a yi salla, wanda,
              Ya bar salla, ya bar rahamu.

San nan azumi na watan Ramala-
              Na, mu yi shi farilla ne gunmu.

Sauran sunna ne in ka yi ka,
              Kyauta wa kanka cikin saumu.

Zakka sai wanda ta cancanta,
              Sai ko mawadaci mai samu.

Da kuɗi, da abinci, da dabbobi,
              A cikinsu ake zakka tamu.

Fasalinta ku tambayi malamai,
               Domin su ne mazowa ilmu.

Aikin Hajji sai ko mai iko,
               Kuma mai guzuri shi zai azamu.

Wajibi ne in da akwai hali,
               Lafiya da kuɗi na zuwa Haramu.

Matalauci shi da marili ba,
               Tilas a wurinsu zuwa Haramu.

Amma yaranmu na zamani,
               Addu’arsu da mu, su fi ƙarfinmu.

Sai suka kurɓi giya, su yi kwaskwas har,
               San nan su yi saje ba game!

Sai girman kai, sai shaƙiyanci,
              Ba su son kishin neman ilmu.

Da yawan ashararanci su ne,
               Daga hotel sai su wuce sanamu.

Su ne manyan ‘ya’yan iska,
               Ba su tarbiyyar neman ilmu.

Ku sani ilmin ga na zamani,
               Shi ne hanyar samun ni’imu.

Shi ke hana tsumma har yunwa,
               Ya hana ka zuwa kwaɗayin laumu.

Ba a aikin banza a Kano,
               Im ba ka kuɗi nemo ilmu.

Ka sani ƙwambonka na banza ne,
              Sai dai a ce ka san ilmu.

Sai mu ɗau takubban yakar ja-
              Hilci ya yi yawa a ƙasashenmu.

Mu sani haka shi ne alheri,
              Mu yi duba nan ga maƙwabtanmu.

Su ne da kuɗi da abinci, tufafi,
              Sun cinye mana ƙarfinmu.

Sai gidan kwano sai motoci,
              Duka ga su tuli a ƙasashenmu.

Wani har tsoronsa mu ke ji,
              Kaito ko jahilci ya cuce mu.

Duka aikin Gwamnati in ka kula,
              Sai ka ga su ne a gaban namu.

Ko a inda En’e akwai nasu,
              Sai ka iske shi ne imamu.

Masu yi musu wanki ko girki,
              Duka yara ne na ƙasashenmu.

In sun najasa su fitar su zubar,
              Domin kwaɗayin neman samu.

Samun izini don ƙasaita,
              Har suna auren ‘yan matanmu.

Kuma ga matansu bila haddin,
              Ba sa yarda da su aure mu.

Mamaki ya hana in yi bayanin
Laifi ne na sakewarmu.

Babban laifi da ya cuce mu,
              Ba ma haɗa kanmu a junanmu.

Kuma dole mu daure wulaƙanci,
               Da takaici gurbin baƙinmu.

Mun ce su ne suka san kome,
              Su ne kunnenmu da bakinmu.

Mu ne raƙuma, su Buzaye,
              Duka inda su ke so sa ja mu.

Lokoto, lokoto, mun miƙa wuya,
              Sai inda su ke son tsaishe mu.

In sun ce nan ne za ku tsaya,
              Kowam motsa ya shafe mu.

Nan za mu tsaya mu yi sauraro,
              Kuma sai sun zo sun tashe mu.

Ga yaƙi ya zo har ɗaka ya,
              Cinye mu da mu da iyalanmu.

Jahilci, lalaci, zalunci,
              Ci uku wanda ya cuce mu.

Duka kun ji muguntar jahilci,
               Kuma za ku ji amfanin ilmu.

Mota, jirgin sama, lantarki,
              Su wayalis ga su ƙasashenmu.

Kome ka gani masana’antu,
              Na Nasara cikinsu akwai ilmu.

Mil dubbai sunka taho suka ci,
               Mu saboda sanin zurfin ilmu.

Har ga wasu ma a maƙwabatanmu,
              Su ke ɗaga hanci sun fi mu.

Har suna tsammani su suka kawo
               Turawa suka mulke mu.

Ilmi ne hasken zamani,
               A ƙasa shi ne akasin zulmu.

A nemi sani har Ingila har,
               A Amirka har Birnin Shamu.

Ilmi ke zayyana ƙuruciya,
              Mun san haka tun kakaninmu.

Al Ilmu yazidul imana,
              Wayazidul sihata fi jisimu.

Wa ya zidul haira alal arali,
              Wa yazidul rizƙa ilal ƙaumu.

Innamal a’amalu binniyyati,
              Jama’a mu yi ƙwazo don kanmu.

Subhanallahi Karimin Sarki,
               Rabbu shi kyautata ƙarshenmu.

Da ma mu cika bisa imani,
              Wa bi jahi Muhammadu Mazonmu.

Tammat baiti saba’in da bakwai,
               Da Mu’azu Haɗejiya yai nazaru.

Manazarta:


NNPC (1982). Waƙoƙin Mu’azu Haɗejia. Northern Nigerian Publishing Company Ltd, Zaria, Kaduna - Najeriya.

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub